Da Ɗumi-ɗumi: Sabon Gwamnan Kogi ya yi muhimman naɗe-naɗe sa’o’i bayan shan rantsuwar kama aiki

Daga BASHIR ISAH

Sabon Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yi wasu muhimman naɗe-naɗe ‘yan sa’o’i bayan shan rantsuwar kama aiki.

Daga cikin waɗanda naɗe-naɗen ya shafa har da Ali Bello wanda aka naɗa a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati.

MANHAJA ta kalato cewa Bello ɗan uwa ne ga gwamna mai barin gado, Yahaya Bello.

Sauran sun haɗa da Folashade Ayodele Arike a matsayin Sakataren Gwamnati, Hilary Ojoma a matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Elijah Evinemi a matsayin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Jerry Omodara a matsayin mai bai wa Gwamna shawara kan tsaro, Isah Ismail a matsayin mai bai wa Gwamna shawar kan sha’anin yaɗa labarai da sauransu.

Bayanai sun ce galibin waɗanda Gwamna Ododo ya naɗa ɗin sun yi aiki da gwamnatin da ya gada ta Yahaya Bello.