Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

A makon da ya gabata, Bankin Duniya ya fitar da rahotonsa kan tabarberewar tattalin arzikin Nijeriya. Rahoto a karkashin duba irin cigaban da Nijeriya ta samu, Cibiyar Hada-hadar Kudi Ta Duniya ta bayyana cewa, tabarbarewar yanayin tattalin arzikin Nijeriya na kara jefa al’ummar kasar cikin wani hali.

Rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya zama annoba ga rayuwar ’yan Nijeriya wanda dole ne hukumomi su yi yaki da hakan. Habakar hauhawar farashin kayayyaki da ke fitowa daga matsalar rashin tsaro, Bankin ya ce, zai iya jefa karin ‘yan Nijeriya miliyan daya cikin matsanancin talauci.

Tabbas tashe-tashen hankulan da hauhawar farashin man dizal, man jiragen sama da alkama duk abin dubawa ne. Yunkurin da farashin man jiragen sama ya yi daga Naira 190 kacal a watan Janairun bana zuwa sama da Naira 800 a yanzu ya sa farashin jiragen sama ya wuce gona da iri. Hakazalika, man dizal da ake amfani da shi wajen sufuri da injinan masana’antu, ya yi tsalle daga farashin kusan Naira 224.9 a farkon shekarar 2021 zuwa sama da Naira 1000 a kowace lita, kuma akwai rahotannin cewa zai iya kaiwa Naira 1,500 kan lita daya nan ba da jimawa ba. Hakazalika, hauhawar farashin alkama ya taimaka wajen hauhawar farashin kayan abinci, tare da sanya abinci wahalar shiga bakunan mutane da dama.

Kafin yakin Ukraine, lokacin da hauhawar farashin kaya a Nijeriya ya kasance daya daga cikin mafi girma a duniya, Bankin ya yi hasashen cewa daga 2020 zuwa 2021, ‘yan Nijeriya kusan miliyan takwas ne za su shiga cikin matsanancin talauci a kasar.

Baki daya, bankin duniya, ya ce, daga shekarar 2020 zuwa bana, ’yan Nijeriya miliyan 15 ne ake tsammanin za su shiga talauci, bisa la’akari da munanan manufofin gwamnatinmu.

A bayyane ya ke ga masu lura cewa, wannan tattalin arzikin yana cikin matsala don haka hauhawar farashin kaya da cututtukan ke qara ta’azzara. Hasashen hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya haura zuwa kashi 17.71 cikin 100 a watan Mayu, bisa hasashen da Bankin ya yi na kashi 15.5 cikin 100 na wannan shekara – wata alama ce da ke nuni da irin givin da tattalin arzikin kasar ya samu. Daga aikin noma zuwa masana’antu, matakin ayyukan da ake aiwatarwa a cikin tattalin arzikin ya kasance cikin mawuyacin hali. Misali a harkar noma, kusan an daina noma a wasu sassan kasar saboda ayyukan ’yan fashin daji da ’yan ta’adda da sauransu.

Matsalolin da aka lissafa a sama ba su ne kadai matsalolin da ke addabar tattalin arzikim kasar ba. Bayan haka, daukacin al’umma na fuskantar wasu matsaloli ko kalubale. Matsalolin kasar nan shi ne yadda ake ganin babu wani abu da ake yi don gano bakin zaren matsalar, da ana tabuka wani abu, a hakikanin gaskiya da za a shawo kan wadannan matsaloli. Abin da kawai mu ke da shi daga ma’aikatun hukuma shi ne kuka daga jami’an gwamnati. Daga kokawar Ministan Lafiya kan yadda yawan al’ummar kasar ke kawo cikas ga ci gaba, sai yadda takwaransa mai kula da harkokin kudi, ke korafin cewa kasar ba za ta iya biyan albashi ba sai ta ci bashi.

Koke-koke ba za su sanya abinci a bakunan mutane ba, kuma ba za su rage farashin kayayyakin da suka yi tashin gauron zabi ba. Lokacin da buqatu ya zarce wadata, dole farashi zai tashi.

Lallai hauhawan farashi wata alaqar tattalin arziki ce; don haka, idan wata kasa tana fuskantar irin wannan hauhawar farashin kayayyaki, yana nuna wani abu ba daidai ba ne ga tattalin arzikin. Za a iya magance wannan babbar matsala ta hanyar kyakkyawan shiri na aiki.

Babban dalilin wannan tabarbarewar tattalin arziki da kuma raguwar jin dadin jama’a za a iya danganta shi da rashin mayar da hankali ga wadanda alhakin su ne sarrafa tsarin. Kowane tattalin arziki yana bukatar kulawa; yana bukatar a sarrafawa. Sai dai akwai kwararan hujjoji da ke nuna rashin mutunta tsarin mulki domin duk ’yan siyasa sun karkata akalarsu ga siyasa da kuma mika mulki ga gwamnati mai zuwa. Ministoci, shugabannin ma’aikatu, da hukumomi a yanzu sun fi zama jami’an fage, yayin da suke yakin neman kuri’u domin samun mukamai a harkokin siyasa na gaba. Duk wadannan ana yin su ne domin cutar da al’umma baki daya.

Wannan jaridar ta yi imanin ya kamata gwamnati ta damu da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. A duk kasar da ake da irin wannan hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin da ke da alaka da su, an rage jin dadin jama’a. Don haka ya kamata gwamnati ta yi gaggawar yin wani abu na zahiri game da hakan.

Muna rokonta da ta zage damtse kan aiki, ta nunawa ’yan Nijeriya cewa ita ce ke kula da tattalin arzikin kasa. Akwai abubuwa guda biyu da za a iya yi don kawar da duk wani tabarbarewar yanayin tattalin arzikin ‘yan Nijeriya.

Gwamnati na iya sakin wani bangare na tsare-tsaren hatsi na kasar a daidai wannan lokaci domin dakile tashin farashin kayayyakin abinci. Haka kuma ya kamata gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su binciko yadda gwamnatocin da suka shude a kasar nan suka yi a lokacin da aka fuskanci irin wannan kalubale. Hakanan za ta iya ayyana dokar ta-baci kan tattalin arzikin da nufin tattara duk albarkatun da ake bukata don tunkarar wadannan kalubalen a gaba.

A yau, manyan bankuna a duk fadin duniya suna cikin tashin hankali, suna daukar matakan da ba a saba gani ba don magance wannan annoba ta hauhawar farashin kayayyaki da yaqin Ukraine ya haifar. Daga Birtaniya zuwa Amurka, Turkiyya, da Brazil, manyan bankuna sun kara yawan kudin ruwa.

Babban bankin Nijeriya ma ya yi haka a kwanan baya inda ya kara kudin ruwa daga kashi 11.5 zuwa kashi 13 cikin dari. Amma yana bukatar yin kari; dole ne ta fito da manufofin da za su magance hauhawar farashin kayayyaki ta la’akari da kebantacciyar kasar. Dole ne a tuna cewa babban aikinsa shi ne tabbatar da farashin da daidaiton farashin canji. Wannan ya fito karara a sashe na 2 (a) na dokar babban bankin Nijeriya, 2007.

To, me ya sa CBN ke nisantar wannan nauyi? Me ya sa ta karkata akalarta ga tallafin wutar lantarki, noma da sauransu? Ba aikin shugaban kasa Bola Tinubu ba ne ya shawo kan hauhawar farashin kayayyaki? Wannan shi ne aikin babban bankin, yana aiki tare da sauran hukumomin gwamnati, ta fuskar daidaita manufofi.

Ya kamata kuma CBN ya sake duba yadda ake bai wa manoman shinkafa rance, bangaren samar da wutar lantarki da sauransu. To amma, idan wadanda suka ci gajiyar kudin suka qi biya a yau, me bankin zai bayar gobe?

Dole ne CBN ta hada kai da dukkan kwararru domin dakile faduwar Naira. Muna kuma roqon shugaban kasa da ya yi kira ga qungiyar tattalin arziki da su gaggauta yin aiki kan wannan lamarin. Tattalin arzikin ya tabarbare kuma dole ne dukkan hannaye su kasance a wuri guda don magance shi.