Ƙona Majalisar Ribas: Kotu ta ɗaure wasu magoyan bayan Fubara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin garkame wasu magoya bayan gwamna Siminalayi Fubara su biyar a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, bisa zarginsu da hannu wajen kona ginin Majalisar Dokokin jihar Ribas da ke Fatakwal, Jihar Ribas.

Mai shari’a Bolaji Olajuwon ya ba da umarnin ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, 2024, jim kadan bayan gurfanar da su a gaban kotu kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi ta’addanci da kisan kai.

Ko da yake sun qi amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake tuhumar su da su, amma alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan yari na Kuje, har sai an saurari bukatar neman belinsu da aka sanya ranar 2 ga watan Fabrairu.
Waɗanda ake tuhuma biyar sun hada da Chime Eguma Ezebalike, Prince Lukman Oladele, Kenneth Goodluck Kpasa, Osiga Donald da Ochueja Thanksgod.

A tuhume-tuhume bakwai, ana tuhumar wadanda ake tuhuma da aikata laifukan ta’addanci ta hanyar mamaye majalisar dokokin jihar Ribas da lalata ta da kona ginin a lokacin rikicin siyasar da ya barke a Fatakwal a watan Oktoban bara.

Bayan zargin Kona majalisar dokokin jihar, an kuma zarge su da kashe wani Sufeto na ‘yan sanda, (SP) Bako Agbashim da wasu ‘yan sanda biyar a unguwar Ahoada na jihar.

’Yan sandan da ake zargin an kashe su ne Charles Osu, Ogbonna Eja, Idaowuka Felix, Paul Victor Chibuogu da kuma Asabar Edi.

Gwamnatin Tarayya ta kuma zarge su da yin amfani da Kungiyoyin asiri daban-daban da suka hada da- Supreme Viking Confraternity, Degbam, Iceland da kuma Greenland wajen tayar da tarzoma a kan al’ummar jihar da harkokinsu na kasuwanci.

Sai dai a lokacin da aka karanta tuhumar da ake musu mai lamba FHC/ABJ/CR/25/2024, duk sun musanta aikata laifin.

Duk da cewa tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ribas, Hon Edison Ehie, ba a sanya shi cikin tuhume-tuhume bakwai na ta’addanci ba, sai dai wani babban Lauyan Nijeriya, SAN, Oluwole Aladedoyin ya wakilce shi a gaban kotu.