Gombe na gab da zarta Kano a fuskar kasuwanci – Adamu Baba

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Bayan dogon nazari da ya yi, fitaccen matashin dan kasuwan nan na Gombe, Alhaji Adamu Baba, sai ya yanke hukunci cewa, Jihar Gombe na gab da kamo Kano wajen kasuwanci, kuma nan da shekaru uku ko biyar masu zuwa, za ta zarta cibiyar kasuwancin ta Arewa.

Dan kasuwar ya yi wannan kiyasin ce da yake hira da  wakilinmu a harabar wajen kasuwancinsa a Gombe City Stores, da ke tsakiyar birnin Gombe ranar Jumma’ar da tagabata, yana mai cewa, “ko shakka babu ganin yadda hada-hadar kasuwanci da cinakayya ke qara bunkasa a kullum a wannan Jihar to nan da shekaru 3 ko 5, ita ce za ta zama cibiyar kasuwancin Arewa.”

Ya kara ba da hujjarsa da cewa, a halin yanzu, Jihar Gombe ta zama matattara da matsugunin dimbin al’ummar Najeriya, yawancinsu ‘yan kasuwa da suka garzayo Jihar daga sassa daban-daban na Arewa da ma kudanci saboda dalilai na rashin tsoron da suka hana su gudanar da kasuwanci a wuraren da suka fiffito, ko kuma don zaman lafiyar da ake da shi a Jihar ta Gombe ba tare da nuna bambancin yare ko addini ba.

“Yau Jihar Gombe ta rungumi ‘Yan Nijeria da dama, mafi yawa ‘yan kasuwa da suke hada-hadar cinikayyarsu a cikin kwanciyar hankali, kuma a kullum, jama’a sai kara tururuwa suke ta yi zuwa cikin Jihar saboda ingantaccen tsaro da kwanciyar hankali wadanda suka tara Gombawa, Hausawa, Fulani, Barebari, Inyamurai (Igbo), Yarabawa, da sauransu ba iyaka duk an hada kai ana ta hada-hadar kasuwanci na yau da kullum a tsanake” inji shi.

Alhaji Adamu Baba a nan, sai ya jinjinawa Gwamnan Jihar, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya da Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar (III) saboda abin da ya kira, kyakkyawar shugabancinsu da kuma kiraye-kirayen da a kullum suke yi wa jama’a da su zauna lafiya, su kuma guji fitina ko tsangwama yana mai lura da cewa, “yau bisa Ikon Allah, ana ta ci gaba da zaman lafiya a Gombe saboda kyakkyawar shugabancin wadannan bayin Allah, kuma kowa shaida ne”

Dan kasuwan mamamlakin Gombe City Stores, wanda yake da kishi ya ga dimbin matasa a Jihar sun rungumi sana’a musamman kasuwanci, ya ce nan ba da jimawa ba, zai kara fadada harkokinsa don horas da matasa kasuwanci saboda rage radadin talauci da kuma kara bunqasa tattalin arzikin Jihar ta harakokin da ‘yan kasuwa suke biya, yana mai farin cikin da cewa, “a yanzu haka, na horar kuma na yaye kusan matasa goma sha biyu”.

Alhaji Adamu Baba sai ya yi kira ga Gwamna Inuwa Yahaya, da ya kara kaimi wajen tallafa wa ‘yan kasuwa a jihar, musamman kanana da masu tasowa domin a cewar sa, “su ne masu kara bunkasa arziki da gina jihar gobe, kuma bana shakka Gwamna zai dube mu, tunda shi ma asalin dan kasuwa ne kafin wannan lokacin, mu dai fatanmu, kada kasuwanci ya fuskanci wani koma baya, sai dai kara cigaba kawai domin alheri ne ga jiharmu da kasa bakidaya,” a cewarsa.