Tarar Kwastom babu-gaira babu-dalili ce babban matsalarmu – Ƙungiyar ’yan kasuwar Arewa

Daga JOHN D. WADA, A Lafiya

A kwanan nan ne  dai wata hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar arewacin kasar nan bakidaya da ake kira Northern Traders Association a turance wadda ta kunshi duka jihohin arewa na kasar nan 19 ta gudanar da wani gagarumin taron ta a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa don tattauna wasu matsaloli da kalubale dake addabar ‘ya’yan kungiyar bakidaya.

A jawabinsa na maraba Shugaban kungiyar na kasa alhaji Baba Usman Jos wanda mataimakinsa Alhaji Jahi Abdullahi ya wakilce shi ya bayyana cewa, kungiyar ta ga ya dace ne ta hada babban taron don samun damar tattauna a kan wasu matsaloli da ‘ya’yan kungiyar ke fuskanta musamman wadanda ke tafiye-tafiye a kan manyan hanyoyin kasar nan don harkarsu ta kasuwanci don kare hakokin su ta hannun ‘yan kwastam da ‘yan sanda da wasu ‘yan bangan hanya dake tsare hanyar suna cin tarar mambobinsu ba gaira ba dalili.

Hakan ya sa Alhaji Baba Usman Jos ya yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga duka gwamnatoti a duka matakai su rika sa ido tare da taka wa wadannan ire-iren hukumomi da ke cin zarafin ‘ya’yan kungiyar da sauran su birki.

Ya ce ba shakka ayyukan kungiyar ta ‘yan kasuwar arewacin kasar nan ta dade tana tallafa wa kokarin gwamnatoti don rage zaman banza da inganta harkokin kasuwanci don bunkasar tattalin arzikin kasar nan bakidaya da sauransu inda ya ce kiran ya zame wajibi idan aka yi la’akari da yadda wadannan hukumomi ke cigaba da taka hakokin mambobin nasu a kowanne lokacin.

Daga nan sai Shugaba Alhaji Baba Usman Jos ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana wasu hanyoyin tara kudaden shiga ga kungiyar kana ya bukaci duka mambobin kungiyar su cigaba da hada kai su kuma rika bin dokokin kungiyar.

Shi ma a nasa bangaren da yake jawabi shigaban tsarawa na kungiyar na reshen jihar Nasawawa wanda shi ne mai masaukin baki wato daya samu wakilcin alhaji Sabo Barau ya gode wa kungiyar dangane da zabin jihar ta Nasarawa a matsayin wajen gudanar da taron a karon nan inda ya ce ba shakka taron bayan gano hanyoyin warware matsaloli da kungiyar ke fuskanta a yanzu zai kuma je nesa ba kusa ba wajen hada kawunan duka mambobinta a arewacin kasar nan bakidaya.

Ya kara da cewa, duk da bai samu damar halartar taron ba a shirye yake ya cigaba da ba da tasa gagarumin gudumawa wajen cigaban kungiyar a kowanne lokacin.  

Shi kuma mai martaba sarkin Lafiya Alhaji Sidi Bage mai ritaya bayan ya jinjina wa hangen nesa da ‘yan kungiyar suka yi na kiran taron ya kuma gode musu dangane da zabin garin Lafiya fadar gwamnatin jihar ta Nasarawa a matsayin wajen taron inda ya tabbatar musu cewa masarautar sa za ta cigaba da ba su cikakken goyon baya don ba su damar gudanar da harkokinsu na kasuwanci yadda ya kamata.

Sauran manyan baki da suka halarci babban taron mai dinbin tarihi sun hada da wakilin kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa da ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa daga ciki da wajen arewacin kasar nan bakidaya inda duk a jawabinsu sunyi fatan alheri ga kungiyar.