Farashin man fetur zai sauka, inji Gwamnan CBN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Farashin man fetur a Nijeriya zai daidaita a bana yayin da matatun mai na gwamnati da na masu zaman kansu suka fara aiki. Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana haka.

Ya yi magana ne a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, a wajen kaddamar da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Nijeriya (NESG) 2024 Rahoton Muhimmanci na Macroeconomic Outlook a Legas.

Mista Cardoso ya ce, ana sa ran daidaitawa ko rage farashin man fetur yana da tasiri mai nisa a sassa daban-daban, yana ba da gudummawa sosai ga ingantaccen tattalin arziki da juriya gabadaya.

Yayin da matatar man Dangote tuni ta fara aikin hakar mai, a na sa ran za a fara aikin matatar man Fatakwal daga yanzu.