Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Babbar Kotun Jiha a Kano ta sanya ranar 4 ga Oktoba, 2022, don gurfanar da ɗan ƙasar Chana nan, Mista Geng Quangrong, bisa zargin kisan gilla ga budurwarsa, Marigayia Ummmulkulsum Buhari, wacce aka fi sani da Ummita, ’yar Nijeriya a Jihar Kano sakamakon rashin bayyanar lauyansa.
Yayin da aka gabatar da ƙarar a ranar Alhamis, Mista Geng, ya nemi kotun da ta ɗage shari’ar don ya sami damar yin magana da lauyansa, wanda zai wakilce shi a gabanta.
Yayin da yake mayar da martani, Kwamishinan Sharia na Jihar Kano, Barista Musa Lawan Abdullahi, bai yi suka game da roƙon na wanda ake ƙara ba.
A cewarsa, “daga dukkan alamu wannan ƙarar ba zai yiwu a yau ba, domin rashin lauyan da zai ƙare wanda ake ƙara, duba da cewa laifin da ake zargin sa da shi babban laifi ne.
“Don haka muna neman a sanya mana gajeren lokaci, domin wanda ake ƙara ya sami damar samun lauyan da zai ƙare shi a wannan shari’a.”
Hakan ya sa alƙalin kotun, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ya sanya ranar 4 ga Oktoba mai kamawa, don gurfanar da wanda ake zargi gabanta.
