2023: An rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

…Yayin da aka ɗage takunkumin yaƙin neman zaɓe
…Na rungumi ƙaddara kan takarar sanata, cewar Ahmad Lawan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da tsare-tsarenta ga masu neman kujerun siyasa daban-daban a babban zaɓen shejarar 2023 mai ƙaratowa, inda ta fitar da ranar Larabar nan da ta gabata 28 ga Satumba, 2023 a matsayin ranar da kowane ɗan takara zai nuna farin jininsa ga al’umma, ma’ana an yarje wa kowane ɗan takara ya fita yaƙin neman zaɓe a jam’iyyu 18 da Hukumar INEC ɗin ta yi wa rajista.

Sai dai ana ganin akwai wasu ƙalubale da idan ba a wayar da kai ko ai ɗauki mataki a kansu da wuri ba, za a iya fuskantar barazana a wajen gangamin yaƙin neman zaven da ‘yan takarkarun za su iya, wanda zai iya shafar lafiya da kuma tattalin arzikin ƙasa.

Saboda haka ne, wani kwamitin wanzar da zaman lafiya a Nijeriya da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Abdulsalam Abubakar da Bishop Matthew Kukah suke jagoranta ya shirya wa ‘yan takara masu neman shugabancin Nijeriya da shuwagabannin jam’iyyu wani taro don rattava hannu kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya domin tunkarar yaƙin neman zaven baɗi.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron rattava hannun akwai: ɗan takarar mataimakin Shugaban Ƙasa na APC, Kashim Shettima da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Labour Party (LP); da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da sauran ‘yan takara.

Rahotanni sun nuna cewa an ƙirƙiri zauren tabbatar da zaman lafiyar ne tun wuraren 2014 saboda hasashen yadda zaɓukan 2015 a lokacin ake ganin kamar yana cike da barazana da ƙalubalen bangar siyasa da dabanci.

Sai kuma ɓangaren jam’iyyu da suka fitar da jadawalin ‘yan kwamitin yaƙin neman zaɓen su tare da wasa wuƙaƙen su na neman yin nasara a zaɓukan da kuma tsara duk wasu dabaru da za su yi kamfe da su, inda wasu jam’iyyun a yayin da aski ya zo gaban goshi sai suke fuskantar rikicin cikin gida musamman Jam’iyyar APC da waɗanda suke ganin ba a yi musu daidai ba wajen saka sunayen ‘yan kwamitin kamfe, inda wasu gwamnonin APC suka yi fatali da shi.

Shi ma Shugaban Jam’iyyar APC Abdulalhi Adamu ya zargi Tinubu da karya alƙawarin da ya yi bisa yarjejeniya kan batun sunayen dakarun kamfen ɗin na shugaban ƙasa.

Cikin wasiƙar da Adamu ya rubuta, ya ce Tinubu ya karya yarjejeniya ta hanyar ƙin saka sunayen Shugabannin Kwamitin Zartaswar APC (NWC) a cikin rundunar kamfen.

Irin haka ɗin ne ya harzuƙa wasu gwamnonin APC har su ka yi barazanar yi wa kamfen ɗin Tinubu ƙafar-ungulu.

Wannan matsaya da gwamnonin APC suka cimma ce ta haifar da dakatar da fara kamfen ɗin APC har sai yadda hali ya yi, domin a shawo kan matsalar.

Yanzu haka ma duk da an fara kamfen tun daga ranar Laraba kamar yadda INEC ta bayar da izini, APC ta ɗage ranar fara kamfen a Jihar Kwara. Sannan kuma shi kan sa Tinubu ba ya ƙasar, ya garzaya Landan.

Cikin wasiƙar da Adamu ya rubuta da kakkausan harshe, ya ce ya yi da-na-sanin jin labarin yadda Tinubu ya watsar da sunayen NWC na APC, aka ware su daga cikin tawagar kamfen.

Adamu ya ce sai da dama ba sau ɗaya ko sau biyu ba, Tinubu ya sha yi masu alƙawarin yin aikin kamfen tare da Kwamitin Zartaswa na APC.

A can baya dai Adamu da Tinubu sun ƙaryata masu cewa akwai saɓani a tsakanin su.

To amma kuma abin da ya faru biyo bayan fitar da sunayen rundunar kamfen ya nuna akwai wata-a-ƙasa a tsakanin su.

Tun da farko dai shi Adamu ya so Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ne aka tsayar takara ba Tinubu ba.

Adamu dai ya rubuta wa Tinubu wasiqa ce a madadin ɗaukacin Kwamitin Zartaswa na APC, wadda ya bayyana cewa ba za su iya yin shiru ba, tilas ce ta sa su rubuta masa wasiƙar.

Ya ce, “sunayen ‘yan kamfen ɗin abin mamaki ne, abin takaici kuma cike ya ke da karya alƙawari da saɓa yarjejeniya da aka yi da Tinubu.”

A Adamu ya fito ɓaro-ɓaro ya tunatar da Tinubu wuraren da su ka zauna ya yi masu alƙawarin a ofishin Adamu da kuma zaman su a ɗakin taro na NWC a Babbar Sakatariyar APC ta Ƙasa, a ranar 7 ga Satumba, 2022.

“Ita fa nasarar zaɓe tilas sai da sa hannun kowa da gudummawar sa ta ke tabbata. Saboda haka kaucewa ko sava alƙawari na iya haifar da shakku ga ‘yan jam’iyya a faɗin ƙasar nan, tun ma tafiya ba ta yi nisa ba.”

Sai dai kuma shugaban jam’iyyar, Adamu ya ƙaryata wannan wasiqa, ya ce ba daga ofishin sa ba ne ta fito.

”Ban san da wannan wasiƙa ba sannan ban san daga inda ta fito ba. Saboda haka ina kira ga ‘yan Nijeriya su yi watsi da haka.

A vangaren ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuwa, wato Alhaji Atiku Abubakar har yanzu ba a samu wani daidaito ba tsakanin sa da Nyesom Wike wanda ake ganin ya zame masa kamar ƙadangaren bakin tulu, inda Gwamna Wike ya yi tsayuwar daka a kan sharuɗansa na idan ana so ya mara wa Atiku baya to lallai sai Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu wanda ya fito daga shiyyar ɗan takarar shugaban ƙasa ya sauka daga kujerarsa, lamarin da ake ganin shi ne ya daɗe bai cinye ba a rikicin cikin gidan PDP, kuma masu sharhi kan lamuran siyasa suke ganin zai ba Atiku ciwon kai wajen yaƙin neman zaɓensa.

To sai dai kuma duk da wancan saka-toka-sa-katsen na cikin gidan jam’iyyar adawar, shi kuwa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo ya kuranta cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar ya fi duka sauran ‘yan takara shiri don tunkarar zaɓe mai zuwa.

Namadi ya bayyana haka ne a wurin taron ƙaddamar da littafi kan Atiku gami da ƙaddamar da kwamitin kamfen ɗin sa.

Namadi ya ce Atiku gogaggen ɗan siyasa ne kuma sannanne wanda ya san matsalolin ƙasar nan da irin alluran da za a danƙara mata ta miƙe faraɗɗaya idan ya zama shugaban ƙasa.

”Atiku ƙwararren direba ne, ba na mota ba kawai, har da yadda za a warware matsalolin da ya dabaibaye Nijeriya, ya san irin giyoyin da zai riƙa danna wa ƙasar ta miƙe samɓal ta hau saiti.

A ƙarshe Namadi ya yi kira ga mambobin kwamitin da su haɗa hannu wuri ɗaya a zo a haɗa kai domin samun nasara a zaɓen.

A ɓangaren sanatoci da ‘yan majalisun tarayya kuwa, wasu sun riga sun yi ɓatan-ɓaka-tan-tan, sun riga sun yi ban-kwana da kujerunsu, wasu kuwa har yanzu akwai shari’un su a gaban kotu.
Sai dai shi Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Ahmed Lawan ya ce ya rungumi ƙaddara hannun bibbiyu, ya karɓi hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta ce ba shi ne halattaccen ɗan takarar majalisar dattijai na Jam’iyyar APC a mazaɓar Yobe ta Arewa ba.

Matakin kotun na zuwa ne kwana guda bayan hukuncin kotun da ke zamanta a birnin Damaturu game da halattaccen ɗan takarar Sanata a Jam’iyyar APC daga mazaɓar Yobe ta Arewa.

Sanatan da kansa ya wallafa bayanin amincewar sa a shafin sa na Tiwita, inda sanarwar ta ƙunshi wani bayani mai alamta yin ban-kwana, inda ya yi godiya ga shugabannin siyasar jiharsa ta Yobe da ma al’ummar mazaɓarsa da ya wakilta tsawon shekaru a majalisun tarayyar Nijeriya.

Hukuncin Babbar Kotun Tarayya ya tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halattaccen ɗan takarar Sanata na Jam’iyyar APC a mazaɓar Yobe ta Arewa.

Tun farko, Jam’iyyar APC mai mulki ce ta miƙa sunan shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan ga hukumar zaɓe a matsayin ɗan takarar sanata mai wakiltar mazaɓar Yobe ta Arewa maimakon Bashir Machina, wanda ya ci zaɓen fitar da gwani na mazaɓar.

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa Abdullahi Adamu ya yi iƙirarin cewa Sanata Ahmad Lawan ya sayi fom kuma ya shiga zaɓen fitar da gwani na Sanatan Yobe ta Arewa, sai dai Bashir Machina ya ce shi kaɗai ya tsaya takara a zaɓen. Sai dai a ranar 21 ga watan Yunin 2022,

Bashir Sheriff Machina ya garzaya gaban kotu, yana ƙalubalantar matakin APC na aika sunan Sanata Ahmad Lawan, a matsayin ɗan takarar sanatanta na mazaɓar Yobe ta Arewa.

Ya dai ce shi ba zai janye wa kowa takararsa ta majalisar dattijai ba. Sanata Ahmad Lawan wanda ya shafe fiye da shekara 20 yana wakiltar al’ummarsa a Majalisar Wakilai da ta Dattijai, ya nemi takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, amma ya yi rashin nasara a hannun Bola Ahmed Tinubu. Kuma tun daga lokacin ne aka fara tababa game da makomar siyasar shugaban majalisar dattijan mai ci.