Batun ’yan ci-ranin Katsina da ke safarar makamai daga Legas yana sosa zuciya

Manhaja logo

Assalam alaikum, ina yi wa Edita barka da wannan lokaci. Allah ya albarkaci kamfanin jaridar Blueprint. Wannan batu da zan yi mahana a kai, batu ne mai sosa rai.

A lokacin da ake faman yaƙi da ta’addanci a Nijeriya, sai kuma ga batun kama waɗansu ’yan ci-rani ɗauke da buhunan albarusai da miyagun awayoyi a wata tashar mota a Jihar Legas a aarshen makon da ya gabata.

Waɗanda ake zargin ’yan Arewa ne kuma suna hanyarsu ne kai makaman zuwa yankunansu; Shin me ya sa suka faɗa wannan muguwar sana’a?

Kuma me ya sa a kullum wasu mutane ba su tunanin Allah ne? Mu sani fa duk abin da ka aikata, za ka tsaya a gaban Allah ranar Ƙiyama.

Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, Kaduna. 08168716583/07014606518.