Gwamnati ce babbar matsalar Nijeriya (3)

Mai karatu barkan mu da sake haɗuwa a cigaba da bayanin kan matsalolin da ke addabar al’ummar ƙasarmu a yau. A wannan mako wanda shine jerin rubutu na uku, zamu duba batun kan yadda mutane ke rasa rayukan su daga ɓangaren gwamnatin.

A harkar tsaro, zamu iya cewa Lahaula, domin duba da irin rayuka da aka rasa. Yau idan ka yi lissafin mutane da suka rasa rayuwar su saboda tashin hankali, yawan su na iya haura Dubu Ɗari (100,000). Wanda cikin su, ’yan ta’adda sun kashe kashi 60, yayin da zamu iya cewa jami’an tsaro ne suka kashe kashi 40. Hakan ya faru ne saboda bude wuta da jami’an tsaro ke yi ma waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

A Borno, an yi wani zamanin da, da zarar Bam ya tashi, maimakon jami’an taso su zo suyi bincike a wurin, kawai sai su buɗe wuta, wanda hakan ya sa mutane da yawa suka rasa rayukan su da sunan Boko Haram alhalin kuma ba haka ba. Kamata ne ace, da zarar Bomb ya tashi, jami’an tsaro, su zo su gudanar da bincike, su duba tayaya Bam ɗin ya tashi. Kuma a duba wani abu na daga cikin Bam ɗin dan a gano, wannan Bam ɗin haɗin gida ne ko na waje?

Idan haɗin gida ne dame dame aka haɗa su. In kuma haɗin waje ne, wa wace kasa aka haɗa Bam ɗin? Idan aka samu sakamakon mai kyau sai a ɗauki mataki na gaba, amman hakan bai yiwu ba. Misalin Abbaganaram da ke cikin Maiduguri, inda nan ne Bam ya fara tashiwa, akwai lokacin Bam ya tashu, sojoji suna zuwa wurin kawai suka buɗe wuta kan kowa. Da masu ceto, da ’yan kallo, duk abin ya shafe su. Har daga baya taymako ya zama wani iri a garin. Idan Bam ya tashi, madadin aje ayi ceto, sai kaga kowa ta kan shi ya ke.

Har ila yau, an taɓa yin wani zamani a Borno, Boko Haram zasu cikin unguwa su kashe mutum, su kuma jami’an tsaro, sai su zagaye unguwar, su kame duk wani na ɗa na miji da ya kai shekara 18 zuwa sama, a tafi dasu wani waje. Za a shafe kusan kimanin a wanni 6 zuwa 7 suna kwance, ana taka su, daga baya mutum ya gama galabaita, sai a sa kowa a layi.

To daman sojoji naɗa wanda suka kama, yana cikin moton su, sai a tambaye shi ko yasan wannan? Sai yace eh shi din boko Haram ne, alhalin ba haka bane, domin ya za’ayi wanda yana jiran mutuwa ko yau ko gobe ya faɗa muku gaskia? Yasan dole kashe shi za a yi, to ba zai yarda ya tafi shi kaɗai ba, sai ya nuna mutane da yawa a tafi da su, akai su gidan yari, babu Shari’a, babu zuwa kotu, shikenan. Wasu sun tafi har yau basu dawo ba.

Bayan nan, akwai abinda ya fi ɓata wa ’yan ƙasa rai, wanda shine, jami’an tsaro za su kama wani, sai su mishi duka, shi ɗin suna masa zargin Boko Haram ne, tabbas haka ne. Kamar yadda na faɗa shi ba zai so ya mutu shi kaɗai ba, sai yayi ta ma sauran mutane da basu boko Haram mugunta.

Su kuma jami’an tsaro sai su kai shi wani wuri da sana’a kawai ake yi, su zagaye wurin, su kwantar da mutane, suna duka, daga baya a sa su a layi, wani daga cikin mota ya riqa nuna su, yana ce wane Boko Haram ne, aka masu, babu Shari’a babu bincike kawai sai a kashe su.

A garin Gwoza jihar Borno, makamancin haka ya taɓa faruwa, an kashe mutane da yawa da sunan Boko Haram, alhakinsu ɗin ba Boko Haram bane. An taɓa yin wani mai suna Auwallu, shi ɗin barawo ne, yana ƙaryar shi ɗan jihadi. Sai ya riƙa zuwa gidan mutane da dare, hana tambayar su kuɗin jihadi.

Wanda ya ba shi ya tsira, wanda kuma bai ba shi ba ya halaka shi. Dubun shi ya cika, ya shiga hannun jami’an tsaro, sai ya ce musu, kar ku kashe ni, nasan ’yan Boko Haram. Tashin farko ya kai su kasuwa layin ’yan nama, an kwantar da mutane daga baya aka kama na kama wa, aka rufe musu idanuwansu, babu bincike, babu zuwa kotu, kawai aka buɗe musu wuta cikin dare. Su ɗin nan iyaye na ga yara ƙanana.

Yaran nan duk sun zama marayu, babu makaranta babu islamiyya, babu mai taymakonsu, babu wanda zai nuna musu hanyar rayuwa. Ba su tsaya iya nan ba, sun riƙa bin unguwa unguwa suna kama mutane suna kashewa. Hakan yasa wasu da yawa suka bar ƙasar ma, wani sanadiyar barin ƙasar kenan saboda hijira da ya yi.

Baya inan ba, hatta ko hari jami’an tsaro zasu kai, mafi yawan mutane da ake kashewa waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba ne. Sai in baki ya yi yawa ka ji sojoji na cewa ayi haƙuri kuskure aka samu. Kamar abinda ya faru a ƙauyen Neja, na buɗe wuta da sojojin sama sukayi kan wa wani ƙauye, yara da mata sun mutu.

Bada komawa ba, bayan faruwan wannan, wani ya sake faruwa a ƙauyen Kaduna, sojoji ne suka buɗe wuta akan muta ne. Don Allah mai karatu ina tsaro a nan? Ta yaya tsaro zai samu? Ta yaya za a tabbatar da tsaro?

Dole sai an samo gwamnati na gaskiya, wanda yasan aikin da yake yi, wanda yasan daga ina ya ke kuma ina zai dosa. Ba ’yan jari hujja ba. Dole sai mun cire ƙabilanci, mun cire son rai. Dole ’yan aasa sun karanci me ke a ina suke, kuma ina za su je.

Ɓangaren jami’an tsaro, ku yi haƙuri fa, ya zama dole na faɗi gaskiya. Domin kuma abin na shafan ku. Zan yi bayani nan gaba.

Wannan kashe-kashe da sojoji ke yi ta ɓangaren gwamnati, sai ya raba kan Musulmai da Kirista. Wasu Musulmai na ganin, ai ’yan sojojin CAN ne keyin wannan kashe-kashen, saboda basa son Musulmai. Wallahi wani har yau wannan batun na tasiri a ran sa, hakan ya sa ya tsani Kiristoci. Daga ɓangaren Kirista kuwa, wasu na ganin ’yan Boko Haram ai Musulmai ne, hakan ya sa suna gaba da Musulmai.

Me ya kamata jami’an tsaro suyi dan ganin an kawo aarshen wannan rikicin? Ya za a yi jami’an tsaro suna daina bada tsoro su zama masu bada tsaro? Mu haɗu a mako na mai zuwa.

Daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected].