Ina roƙon ku yafe wa Gwamnatin Buhari, cewar Aisha ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Uwargidar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta roƙi ‘yan Nijeriya su yafe wa Shugaba Muhammadu Buhari kan tsadar rayuwa da matsalolin tsaron da suke fuskanta ƙarƙashin gwamnatinsa.

Ta ce, “Mai yiwuwa mulkin bai zama kamili ba, amma ina amfani da wannan dama wajen roƙon yafiyar malamai da da ma al’ummar Nijeriya baki ɗaya. Akwai buƙatar mu haɗa hannu mu yi aiki tare don samun ingantacciyar Nijeriya.

Aisha ta yi waɗannan kalaman ne yayin addu’o’i na musamman da aka yi wa Nijeriya yayin sallar Juma’a a ranar Juma’ar da ta gabata albarkacin cikar ƙasar shekara 62 da samun ‘yan cin kai.

Ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dage da addu’ar Allah Ya sa a yi zaɓe da kuma miƙa mulki lami lafiya a 2023 idan Allah Ya kai mu.

Ranar 1 ga watan Oktoban duk shekara Nijeriya ke bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya, wanda a bana ranar ta faɗa a Asabar da ta gabata wanda ke nuni da cikar ƙasar shekara 62 da samun ‘yancin kai.