Ajandar ’yan takarar shugaban ƙasa

A ranar 28 ga Satumba, 2022 ne aka fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a hukumance.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), a baya-bayan nan, ta fitar da sunayen ’yan takara 18 da ta wanke don tsayawa takara. Sun haɗa da ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar; jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi; jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Alhaji Musa Kwankwaso da sauransu.

A bayyane ya ke cewa Obi, Atiku da Tinubu ne ke kan gaba a zacen da ke tafe. Kowanne daga cikinsu zai iya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a shekarar 2023. Amma bayan kurari da alƙawuran da za su biyo bayan yaƙin neman zaɓe, akwai manyan qalubale masu zurfi da ke tunkarar ƙasar, waɗanda ake sa ran ’yan takarar za su magance.

Daga cikin su, babbar matsalar ita ce rashin tsaro. Kamar yadda ya ke a yanzu, kusan kowane ɓangare na ƙasar ba shi da tsaro. Daga Sakkwato zuwa Maiduguri, Kaduna zuwa Binuwai, Imo zuwa Anambra har ma da Ondo zuwa Ogun, ’yan bindiga da ’yan ta’adda ne ke riƙe da madafun iko. Ko ina da alama ana cikin firgici da fargaba.

Ɗaliban da ba su ji ba, ba su gani ba, ba su tsira ba domin su ma suna faɗawa cikin tarkon garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan, musamman a Arewa. Duk da waɗannan matsaloli, gwamnatin yanzu ba ta tashi haiƙan wajen magance matsalar tsaro da gaske ba.

Kwanan nan, Shugaba Muhammdu Buhari ya umurci sojojin ƙasar da su kawo ƙarshen ƙalubalen tsaron ƙasar nan da watan Disamba na shekarar 2022. Ba a da tabbacin yadda za a cimma hakan cikin ƙanƙanin lokaci. Muna sa ran ’yan takarar shugaban ƙasa za su gaya mana yadda za su tunkari wannan dodo a Nijeriya.

Muna kuma sa ran za su gaya mana yadda za su gyara tattalin arzikin ƙasar nan. A halin yanzu, Nijeriya ita ce hedikwatar talauci a duniya inda kusan miliyan 100 daga cikin sama da miliyan 200 ke rayuwa cikin ƙangin talauci. Rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki sun haɗa kai suka yi mummunar illa ga ‘yan Nijeriya musamman matasa.

Yayin da a halin yanzu rashin aikin yi ya kai kashi 33 cikin 100, hauhawar farashin kayayyaki, musamman hauhawar kayan abinci, ya haura shekaru 17 zuwa kashi 20.5 cikin 100 a watan Agusta. Naira ta yi sama haiƙan, domin kuwa bashin da ake bin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 42.85. Manazarta sun yi kiyasin cewa zai iya kaiwa Naira tiriliyan 60.9 a shekara mai zuwa.

Wasu daga cikin ‘yan takarar sun nuna zimmar gyara tattalin arzikin Nijeriya. A wani taro na baya-bayan nan da ƙungiyar ’yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta shirya, duka Atiku da Obi sun sanar da ‘yan Nijeriya yadda suke da niyyar tunkarar ƙalubalen tattalin arzikin ƙasar idan aka zaɓe su a matsayin shugaban ƙasa.

Muna dakon jin tsarin sauran ‘yan takara. Muna kuma so mu san, alal misali, yadda za su magance matsalolin da ke tattare da kiwon lafiya da ilimi. Halin da makarantunmu ke ciki dai shi ne yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi.

Yajin aikin da ƙungiyar ta fara a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, ya gurgunta ayyuka a manyan jami’o’inmu. Cibiyoyin lafiya ba su da kyau saboda likitoci su ma sun sami dalilin fara yajin aiki a lokuta da yawa. Dubban likitocin ne suka yi hijira zuwa ƙasashen waje domin neman wuraren aiki saboda kuɗin da ake biyansu a ƙasar ba ta ishensu.

A yayin da masu kuɗin ke tafiya ƙasashen waje domin jinyar ƙananan cututtuka, talakawan Nijeriya da dama na ci gaba da mutuwa saboda rashin kyawun wuraren kiwon lafiya.

’Yan Nijeriya kuma suna son sanin yadda ’yan takarar ke da niyyar mayar da kowane ɓangare na ƙasar yadda yakamata. Babu shakka kawunan ’yan Nijeriya ya rabu a yanzu fiye da kowane lokaci.

Yawancin mutane suna karkata zuwa ga ɗan ƙabilarsu ko addininsu a wannan zamani. Tun kafin a fara kamfen a hukumance, an sha yin kalaman ɓatanci a wasu sassan. Wannan na iya kawo nakasu ga ƙasar.

Babu shakka aikin da ke gaban shugaban Nijeriya mai jiran gado yana da girma sosai. Ba aiki ba ne ga mai rauni. Don haka, yaƙin neman wannan matsayi ba zai iya zama kasuwanci kamar yadda aka saba ba. Ba kuma zai zama liyafar shan shayi ba.

‘Yan Nijeriya sun yi ta sa ido kan wannan lokaci. Suna sa ran ‘yan takarar za su samar da mafita mai amfani ga ƙalubalen ƙasar. Magana yana da arha. Don haka, bai kamata a yi magana kawai ba. Kowanne daga cikin ‘yan takarar ya kamata ya ba da misalai masu amfani da takamaiman lokacin da za a magance su.

Zarge-zargen juna ba shine abin da ‘yan Nijeriya ke son ji a yanzu ba. Wannan lokacin ya ƙare yayin da yawancin masu jefa ƙuri’a suka nuna sun fi hikima. Sun nuna sun gaji da yaudarar ‘yan siyasa da tsarin gaba ɗaya. Kafofin watsa labarai suna da muhimmiyar rawar da za su taka a wannan lokacin.

Ba wai kawai ta tsara ajanda ne kawai ba, dole ne ta sanya ido tare da ɗaukar nauyin ‘yan takara ga al’ummar Nijeriya. Dole ne kuma kafafen yaɗa labarai su yi taka-tsan-tsan wajen yaɗa munanan kalamai ko kalaman qiyayya ko dai ta ’yan takara ko magoya bayansu.

Shekara mai zuwa za ta zama sabuwar fari ga Njjeriya. Wace niyya ‘yan takarar suke da shi ga Nijeriya? Ta yaya suke da niyyar ceto ƙasar daga zimbin matsalolin da suka dabaibaye ta? Waɗannan su ne tambayoyin da ya kamata su mamaye zukatanmu yayin da muke shiga lokacin yaƙin neman zaɓe.