Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani lamari mai cike da ruɗani ya ɗauki hankalin jama’a a kafafen sada zumunta, bayan wata mata ta jefa mijinta cikin babbar asarar kasuwanci har ta kai Naira biliyan 7.8, sakamakon zargin cin amana a aurensu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya fara ne bayan matar ta lura mijinta na yawan mu’amala da wata lamba a wayarsa, lamarin da ya sa ta zargi cewa yana hulɗa da wata mace a ɓoye.
Wannan zargi ne ya sa ta ɗauki mataki cikin gaggawa ta hanyar gogewa don katse hulɗa da wannan lambar, ba tare da cikakken bincike ba.
Sai dai daga baya an gano cewa lambar da matar ta ɗauka a matsayin wata mace, a zahiri ta wani muhimmin abokin hulɗar kasuwanci ne, wanda ke da alaƙa da wata babbar yarjejeniya da mijin ke ƙoƙarin kammalawa tsawon lokaci.
Wannan mataki da matar ta ɗauka ya katse mu’amala tsakanin mijin da abokin kasuwancinsa, wanda hakan ya janyo rugujewar yarjejeniyar da kuɗinta ya kai naira biliyan 7.8.
Hakan ya haifar da babbar asara ga mijin tare da janyo muhawara mai zafi a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta.
A cikin bidiyon da ya bazu, an kuma ga yadda mijin cikin fushi ya riƙa dukan matarsa, abin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a tare da jawo suka daga ɓangarori daban-daban.
Wasu daga cikin masu sharhi sun ɗora laifi kan matar bisa yin gaggawar ɗaukar mataki ba tare da hujja ba, yayin da wasu kuma suka jaddada muhimmancin amincewa, haƙuri da kuma sadarwa mai kyau a tsakanin ma’aurata domin kauce wa irin wannan mummunan sakamako.
A gefe guda, wasu sun yi Allah wadai da dukan matar da mijin ya yi, suna mai cewa babu wani uzuri da zai sa a yi amfani da tashin hankali a cikin aure, duk da irin matsin lamba ko fushin da mutum ke ciki.
Lamarin ya zama darasi ga ma’aurata kan muhimmancin fahimtar juna, gujewa zargi maras tushe, da kuma sarrafa matsaloli cikin hikima domin kare dangantaka da kuma kauce wa asarar da za ta iya zama babba fiye da tsammani.
