

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gidauniyar ‘British American Tobacco Nigeria Foundation’, BATN tare da haɗin-gwiwar Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya da Ma’aikatar Noma da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Zamfara, sun bai wa mata 200 da jariran kajin turawa don inganta shirin kiwon kaji a jihar.
A lokacin da ya ke magana a wajen ƙaddamar da rabon kajin a Gusau, babban Manajan BATN, Oludare Odusanya ya ce, gidauniyar ta zaɓo mata 200 ne daga dukkan ƙananan hukumomi 14 dake jihar don su ci gajiyar tallafin.
Ya ce kowacce mace za ta karɓi kaji guda 20, buhun abincinsu na musamman da kuma muhimman bitamin don tallafa wa kiwon kaji mai ɗorewa a jihar.
“Muna nan jihar Zamfara ne domin aiwatar da aikin kawo sauyi da aka tsara domin inganta rayuwar mata da inganta rayuwar karkara a jihar kuma muna da yaƙinin cewa, ta hanyar saka hannun-jari acikin al’ummarmu musamman a hannun mata da kuma sana’o’in hannu, mu na dasa iri ne.”
“Wannan yunƙurin ba wai don samar da albarkatu ba ne kawai ba, yana nufin samar da ci-gaba, da ƙarfafa tattalin arziki a tsakanin al’ummominmu”, inji manajan.
Ya kuma ce, kiwon kaji ya fito ne a matsayin sana’ar kawo sauyi, ba wai kawai tushen samun kuɗin shiga ba, har ma da samar da abinci mai gina jiki da kuma ƙarfafa haɗin kan al’umma.
Kazalika, manufar kafa gidauniyar ita ce ƙarfafa wa mata gwiwa tare da ba su kayan aiki da ilimi domin kafa sana’o’i masu inganci da za su taimaka wajen ci-gaban al’umma.
Ya yi nuni da cewa gidauniyar ‘British American Tobacco Nigeria Foundation’ tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2002 ta ke tallafa wa gwamnatin tarayya da na jihohi wajen gudanar da ayyukan bunƙasa noma tare da kashe sama da Naira biliyan 4 wajen tallafa wa ƙananan manoman karkara.
“Ya zuwa yanzu, mun kai sama da mutane miliyan 1.3 da suka ci gajiyar tallafin, kuma muna sa ran za mu ruɓanya hakan nan da shekaru 10 masu zuwa ta hanyar ƙara tallafi ga ƙananan manoma a faɗin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.”
Da take kaddamar da shirin, uwargidan gwamnan jihar, Hajiya Hurriyya Dauda Lawal, ta yaba wa gidauniyar ta samar da tabar sigari ta ƙasar Britaniya bisa tallafin da take bai wa mata a jihar.
Ta ce wannan sabuwar dabarar za ta bai wa matan da suka ci gajiyar shirin kiwon kaji damar zama masu dogaro da kansu.
Ta buƙaci matan da suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da kajin da aka ba su yadda ya kamata.
Hajiya Hurriyya ta bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Mai gidanta za ta ci gaba da haɗa kai da duk kungiyoyin da suka dace wajen bunƙasa jihar.
