Ko Ƙasar Japan take son taimaka wa Afirka cikin sahihanci?

Daga CMG HAUSA

An gudanar da taron raya ƙasashen Afirka karo na 8 da ƙasar Japan ta jagoranta a ƙasar Tunusiya daga ranar 27 zuwa ta 28 ga wata.

Ko dai rahotannin kafofin yaɗa labarai na kasar Japan ko kuma sauraron jawabai daban-daban da jami’an ƙasar Japan suka gabatar a yayin taron, wani abin da ake ji shi ne, a cikin alƙawuran “taimakawa” Afirka da ƙasar Japan ta ɗauka, ana ganin yadda ƙasar Japan ta saka wasu abubuwan son kai nata a ciki, har ma ba zato ƙasar Sin ta zama wani jigon da ƙasar Japan ta kan ambata a yayin taro, ko da yake ƙasar Sin ba ta halarci taron ba.

A yayin taron, firaministan Japan Fumio Kishida ya sanar ta kafar bidiyo cewa, a cikin shekaru 3 masu zuwa, ƙasarsa za ta zuba jarin dalar biliyan 30 a ƙasashen Afirka, sannan za ta horas da ƙwararrun nahiyar dubu 300 da dai sauransu.

Fumio Kishida ya jadadda cewa, “Wannan aiki ya sha bamban da na ƙasar Sin”.

Jaridar Asahi Shinbunmafi, wato jarida mafi karɓuwa a ƙasar Japan ta bayyana a cikin rahoton da ta wallafa a ranar 28 ga wata, cewar firaminista Fumio Kishida ya jaddada dangantakar dake tsakanin Japan da ƙasashen Afirka ne domin yana son rage tasirin ƙasar Sin a Afirka kawai.

A matsayinta na ƙasar da ta sha kaye a yaƙin duniya na biyu, kodayake yanzu ƙasar Japan ƙasa ce mai arziki a duniya, amma ba ta son zama mai ƙarfin tattalin arzki kawai, ta dade tana ƙoƙarin neman samun matsayi na siyasa a duniya.

Zama wata mambar dindindin a kwamitin sulhu na MƊD, wata muhimmiyar hanya ce gare ta wajen cimma wannan buri.

A ’yan shekarun baya-bayan nan, a kullum ƙasar Japan ta yi amfani da manyan tarukan ƙasa da ƙasa iri iri, kamar taron raya ƙasashen Afirka, ta ce, yin gyare-gyare a kwamitin sulhu na MƊD shi ne manufa ce ɗaya ta Japan da ƙasashen Afirka.

A yayin taron na wannan karo, Japan ta sake gabatar da wannan ra’ayinta, kuma ta sake bayyana yunkurinta na ɗaukar ƙasashen Afirka a matsayin “Gidan ƙuri’o’i” da kuma za ta gindaya sharuɗɗan siyasa a lokacin da take samar da agaji.

Fassarawar Safiyah Ma