Tashar bincken sararin samaniyar ƙasar Sin ta sanar da sabon ci gaba a gwajin kimiyyar rayuwa

Daga CMG HAUSA

Tashar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin, ta cimma wani sabon ci gaba a aikin kimiyyar rayuwa, wanda ke lura da yadda irin shuka daban-daban suke girma a sararin samaniya.

Samfuran nau’o’i irin shuka guda biyu, wato furen “thale cress” da shinkafa, sun kasance a ɗakin gwaji tun ranar 28 ga Yuli.

An yi amfani da irin furen “thale cress” a zaman samfurin ƙwayoyi don gudanar da bincike na tushe.

Cibiyar nazarin kimiyya ta ƙasar Sin (CAS) ta bayyana a wani taron manema labarai da ta kira jiya cewa, gwajin dashen “thale cress” da shinkafa da ke cikin na’urar bincike ta Wentian na ƙasar Sin, na ci gaba da tafiya yadda ya kamata.

Ya zuwa yanzu, furen “thale cress” ya fitar da ganye hudu. Yayin da girman nau’in shinkafa mai tsayi ya kai tsayin kusan santimita 30, kana girman nau’in gajeriyar shinkafar ta kai kusan santimita 6.

A cewar Zheng Huiqiong, wata mai bincike a cibiyar CAS, da ta kware a fannin kimiyyar ƙwayoyin halitta, gwaje-gwajen guda biyu, za su fayyace yanayin rayuwar kowace shuka a sararin samaniya da kuma gano yadda ake amfani da yanayin da ake kira microgravity, don shuka tsirran da kuma ƙara ƙarfin samar da shuke-shuke a sararin samaniya.

Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya