Ko namiji aka ci zarafinsa za mu tsaya ma shi – Hannatu Muhammed 

“Dalilin shugabancina mata sun samu ‘yanci a Katsina”

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hajiya Hannatu Muhammed ita ce Shugabar ƙungiyar Mata ‘Yan Jarida Reshen Jihar Katsina, wato NAWOJ, a halin yanzu ita ce mataimakiyar babban manja na gidan talabijin na ƙasa, wato NTA da ke Katsina, ta yi fice a fannoni da dama kama daga gabatar da shirye shirye a gidan talabijin, bai wa mata shawara game da yadda zasu kyautata zamantakewa da iyalansu. Kazalika fitacciyar ‘yar jaridar ta kasance ‘yar gwagwarmaya da ke wayar da kan mata don su fuskanci ƙalubalen rayuwa da ke gabansu.

Wakilin Manhaja a Katsina Umar Garba ya tattauna da Hannatu Muhammed game da batutuwan da suka shafi aikinta na jarida, bai wa matasa maza da mata shawara, cigaban da ƙungiyar NAWOJ ta samu a Katsina da dai sauran batutuwa.

MANHAJA: Masu bibiyar Manhaja za su so jin taƙaitaccen tarihinki?

HANNATU: Assalamu alaikum, da farko sunana Hannatu Muhammed ni ‘yar asalin Jihar Katsina ce kuma ni ‘yar jarida ce, na yi karatun primary school a Aunty Ramatu primary and secondary school Katsina, sannan na yi secondary school a Police Secondary school, Minna. Bayan nan na yi IJMB a Isa College of Education sannan na yi karatun digiri ɗina a Bayero Uniɓersity Kano inda na karanta B.A Hausa. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihina.

Na fara aiki a NTA Hediƙuaters da ke Abuja bayan kamar wata shida ina aiki a can sai na dawo NTA Katsina, har yanzu ina nan a NTA Katsina. A halin yanzu ni ce Assistance Manager, kuma muna fatan mu zama manajoji nan gaba kaɗan idan Allah ya yarda, bayan nan ni ce shugabar ƙungiyar mata ‘yan jarida wato NAWOJ reshen Jihar Katsina.

A matsayinki ta shugabar ƙungiyar mata ‘yan jarida a Katsina, wane cigaba ƙungiyar ta samu a ƙarƙashin jagorancinki?

To Alhamdulillahi da farko dai sadda na fara aikin jarida a Jihar Katsina na kai wurin shekara shida ban ma san akwai wata ƙungiya da ake kira NAWOJ ba, wato ƙungiyar mata ‘yan jarida sai daga baya aka ga yakamata muma NTA mu shigo a riƙa damawa da mu cikin ƙungiyar, mun je taron NAWOJ na farko inda muka samu ƙungiyar na cikin rigingimu a lokacin mun samu shugabar ƙungiyar wadda shekararta 30 ita ke shugabancin ƙungiyar, kowa ya san a ƙa’ida ba haka ake yi ba to a lokacin shine aka ce mana mu da muka je daga NTA me muke ganin zai kawo masalaha cikin ƙungiyar sai muka ce mu dai a yanzu baza mu iya shugabanci ba, saboda ba mu san komai game da ƙungiyar ba amma mun yarda mu zama mambobi daga baya mambobin ƙungiyar suka ce ba wadda suke so ta zama shugabarsu sai ni sai dai ban so haka ba saboda ban cika son shugabanci ba, saboda ina tunanin yadda za ka yi wa kowa adalci haka dai aka tursasani tun daga nan har zuwa matakin shugabanci na ƙasa, ta haka Allah ya sa ni ce shugabar. Alhamdulillah tun da na zama shugabar ƙungiyar mata’yan jarida na kawo cigaba mai yawa cika hadda training (horarwar sanin makamar aiki) ga mata ‘yan jarida, wani lokaci ma idan na samo damar training ga matan na kan saka hadda maza don su amfana da horon da za a bayar, sannan dalilin shugabaci na mata sun samu ‘yanci a Jihar Katsina.

A matsayinka na ɗan uwa abokin aikina, kun san irin gwagwarmayar da muke yi idan aka take haƙƙin mace mu kan tabbar da cewa mun ƙwato mata haƙƙinta duba da cewa a nan Arewa har yanzu karatun yara mata shine baya an fi bai wa na maza muhimmanci, ƙoƙarin ƙungiyarmu shine matan ma a ba su damar yin karatu kamar yadda idan kana da ɗa namiji idan ka kai shi makaranta ita ma ‘ya mace a bata irin wannan gatan, wayar da kai da muke yi na yin tasiri sosai saboda haka yanzu a Jihar Katsina da wuya ka ga ana cin zarafin mata ko a wurin aiki ko wani wurin na daban.

Ko da muke mata, ina da miji, ina da uba, ina da ɗan uwa sannan a wurin aiki waɗanda aiki ya haɗa mu sun zama ‘yan uwa ka ga ai bana so a ci zarafinsu, ba ka san akwai yadda ake cin zarafin maza ba saboda haka ko namiji aka ci zarafinsa zamu tsaya ma shi don mu tabbatar ya samu adalcin da ya kamata, kamar yanzu muƙaman gwamnati da ake bada wa abinda ya sa muke so mata su samu irin wannan dama saboda an ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne duk irin wannan na cikin cigaban da muka kawo don ganin muryar mata ta kai inda ya kamata ta kai.

A ganinki mata ‘yan jarida na taka rawar da ya kamata su taka kamar takwarorinsu maza a fagen yaɗa labarai?

Mata ‘yan jarida na bakin ƙoƙarinsu kuma idan aka bamu dama za mu iya taka muhimmiyar rawa, amma kamar a Arewacin Najeriya za ka ga har yanzu akwai abubuwan da ba a barin mace ta je ta yi da mace ta yi yunƙurin yin wani abun sai a ce aikin namiji ne, idan mun yi nisa bai wuce ma’aikatu irinsu ma’aikatar mata ko ma’aikatar ilimi, ba kamar takwarorinmu na ƙasashen waje ba irinsu Christiane Amanpour ai mace ce ‘yar jarida filin yaƙi take zuwa don ɗauko rahotanni na tabbata anan ma idan za a bamu dama za mu iya akwai lokacin da nike interɓiew da wasu mutane nike gaya masu cewa, idan aka ban dama ni ma zan iya zuwa na ɗauko rahotanni muddun zan samu kariyar da ya kamata na samu. Matsalar su kansu maza  idan za a tura su fagen yaƙi babu kayan kariya irinsu ‘bullet proof’ da za a ba su to ba a bamu dama saboda a cikin mambobi na akwai ‘yan jarida mata da ke ƙorafin ba a ba su dama su je wasu wuraren don gudanar da aikinsu sai dai a riƙa kai maza.

Alhamdulillah sunan ‘yan jarida mata ya canza a halin yanzu, saboda a da idan aka ga mace ‘yar jarida kallon mara mutunci ake mata amma yanzu iyaye da kansu suke gaya min cewa suna so ‘yayansu mata su zama kamar ni a aikin jarida saboda mutane sun fara gane ‘yar jarida zata iya ƙwato maka haƙƙin da babu wanda zai iya ƙwato maka, idan ka duba a yanzu mafi yawan ‘yan jarida a Katsina matan aure ne kuma masu kamun kai da kama mutuncinsu, amma bance babu ɓata gari ba amma kullum abinda muke gaya wa mambobinmu shine za ki iya yin suna na mutunci a wannan aikin kuma za ki iya yin sunan da ba na mutunci ba. 

Akwai shugabanninmu mata da ke ba mu shawara kada mu bi irin hanyar da suka bi lokacin da suke aiki don su yi suna saboda haka ina ganin idan aka bamu dama za mu iya yin abinda ƙila kuma mazan ba za ku iya yi ba.

A wasu jihohin mata ‘yan jarida na ƙorafin cewa, ƙungiyar NAWOJ na nuna bambanci a tsakanin mambobinta wajen tafiyar da ƙungiyar ana samun irin wannan ƙorafin a Katsina?

A matsayi na, ta Chairperson women journalists idan wani ya kira ni daga wani wuri ya ce yana son na taimaka ma shi da ‘yar jarida ɗaya wadda zata je wuri kaza ko ta yi wani aiki iri kaza wallahi wata yarinya ce zan tura saboda na aminta da aikinta kuma baza ta sa na ji kunya ba ka cire son kai saboda haka kaga kuwa mata na ƙoƙari a aikin nan su ma waɗanda basa ƙoƙarin muna ƙoƙarin ganin mun jawo su a jiki.

A NAWOJ ta Jihar Katsina muna ƙoƙarin ganin mun yi wa kowa adalci shiyasa na ce maka lokacin da na fara shugabancinta na zo na samu rigingimu da yawa, saboda haka na yi ƙoƙarin ganin na daidaita irin waɗannan matsalolin da ake fuskanta ba wani abu ke haddasa matsaloli a ƙungiya ba kamar abaka wani abu ka raba amma ka cinye  ko kuma a samu wasu damarmaki da za a bai wa mambobin ƙungiyar amma ka ƙi ba su damar, ko kuma ka kai naka wani ƙorafin ma da ake samu wani wajen shine idan aka buƙaci ‘yan jarida mata wasu wuraren sai wasu shugabannin su kai mata ‘yan gidansu waɗanda ba ma ‘yan jaridar ba ne.

Idan aka samu dama kamar ta bayar da training ga mata ‘yan jarida idan na tura wata a wannan karon idan kuma aka sake samun wata damar sai na tura wata, ko uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya idan aka tura ki training to baza a sake tura ki ba sai dai a tura wata ko wasu, ko kuma sai an sake zagayo wa kanki. Wani lokaci ma damarmaki da ake ba ni sun yi wa mambobi na yawa, a baya ma na kan haɗa da mazan saboda idan wani ɗan jarida ya yi ba dai-dai ba ai za a ce daga Katsina ya ke shiyasa nake tafiya da kowacce mamba tare don dai a ma kowa adalci.

Akwai mata da suke sha’awar yin aikin jarida, ƙila za su ga wannan hirar ta mu ta ya za su iya shiga aikin?

Aikin jarida yana da matuƙar muhimmanci a tsakanin al’umma shiyasa akwai abinda ake ce ma ‘ethics of journalism’ to daga ranar da ka bar ɗaya ka sauka daga kan aikin, saboda haka duk wadda ke son shiga aikin jarida sai ta nemi ilimi ta yi ƙoƙarin ganin ta karanta Mass Communication ko kuma taje wata makaranta ta karanta Journalism karatun ne zai bata damar sanin abinda ya kamata ta sani a aikin sai kuma ta yi ƙoƙarin samun training (horo) game da aikin jarida idan ta yi haka zata samu certificate (shaidar karatu) mai kyau daga nan kina da damar da za ki nemi aikin jarida, aikin jarida yana da daɗi idan kin yi karatu saboda yanzu aikin jarida ya wuce ka je gidan radiyo ko talabijin kai aiki yanzu duk wata ma’aikata da ka sani sai ta ɗauki ɗan jarida a Communication department ɗinta, idan yau ka zama gwamna kana son ka ɓata mulkinka to ka ɗauki wanda bai san aikin jarida ba ka ba shi Commissioner of Information. Ina gaya maka baza ka taɓa samun abinda kake so ba saboda sai kana da ilimin aikin jarida zaka iya zaɓar kalmomi idan baka da ilimin zaka iya faɗar abinda zai kawo matsala a cikin al’umma.

Na tuna lokacin da aka yi cutar Korona, a nan Katsina akwai wani Press Release ( Sanarwa) da gwamnati ta saki amma kwata kwata kowa ya kasa gane wane saƙo gwamnatin ke son isar wa al’umma abinda mutane suka fahimta daban da abinda gwamnati ke nufi sanadiyyar haka aka riƙa kama mutane, saboda mutanen ba su san abinda ake nufi ba wata ƙila wanda ya fitar da Press release ɗin ba ɗan jarida ba ne ni kaina da nike ‘yar jarida ban fahimta ba to ta ya wanda ba ɗan jarida ba zai fahimta saboda haka karatun dai shine farko idan an gama sai a nemi aiki, aikin jarida kamar jihadi ne za ka iya samun lada a ciki kuma za ka iya samun zunubi.

Banda kasancewarki fitacciyar ‘yar jarida shin ko akwai wata sana’a da kike yi ta daban?

Za mu kwana a wannan tambayar, wadda da yardar mai dukka a mako mai zuwa, baƙuwarmu za ta amsa mana kafin wasu tambayoyin su biyo baya.