Kolmani: Jami’ar NEU Gombe ta rage kuɗin karatun kwasa-kwasai shida da kashi 50

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Jami’ar North-Eastern University, Gombe (NEU Gombe), ta sanar da tallafin karatu na kashi 50 cikin 100 ga ɗaliban da za su yi karatun digiri a kwasa-kwasai shida na kimiyya, a wani shiri da ta ce zai taimaka wajen shirya matasa domin cin moriyar sabbin damarmakin da ake samu a fannin man fetur da iskar gas.

Shugaban jami’ar kuma wanda ya kafa ta, Dakta Sani Jauro (Dan Lawan na Gombe), ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye ɗaliban Pen Resources Academy na shekarar 2026 da aka gudanar a Gombe.

Ya ce shirin tallafin na daga cikin matakan da jami’ar ke ɗauka domin bai wa matasa damar samun ilimin da ya dace da sauye-sauyen tattalin arziki da ake samu, musamman sakamakon ayyukan binciken man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Gombe da Bauchi.

Kwasa-kwasan da tallafin ya shafa sun haɗa da Petroleum Chemistry, Environmental Management and Toxicology, Industrial Chemistry, Microbiology, Biotechnology, da Urban and Regional Planning.

Jauro ya yi kira ga ɗaliban da suka kammala karatu da sauran matasan da ke shirin neman gurbin karatu da su yi amfani da damar, yana mai cewa bunƙasar fannin man fetur da iskar gas a Arewa maso Gabas za ta ƙara buƙatar ƙwararrun ma’aikata masu ilimin kimiyya da fasaha.

Ya ce NEU Gombe na ƙoƙarin daidaita shirye-shiryen karatunta da buƙatun kasuwar ƙwadago domin ɗalibai su samu ilimin da zai taimaka musu wajen samun aikin yi da kuma kafa sana’o’insu.

“Muna son tabbatar da cewa ɗalibanmu ba wai sun samu cancantar karatu kawai ba, har ma sun samu ilimin aiki da ƙwarewar sana’a da ake buƙata domin su yi gogayya a kasuwar ƙwadago,” in ji shi.

Ya kuma bayyana shirin jami’ar na kafa cibiyar bunƙasa ƙwarewa a fannin man fetur da iskar gas (Oil and Gas Competency Development Centre), wadda za ta mayar da hankali kan horar da ɗalibai da ƙwararru a fannoni masu alaƙa da masana’antar.

A cewarsa, cibiyar za ta yi aiki tare da ƙungiyoyin da ke bayar da takardun shaidar ƙwarewa da ake amincewa da su a duniya, domin bai wa masu cin gajiyar shirin damar samun ƙwarewar da za ta ƙara musu damar samun aikin yi.

Jauro ya ce tallafin kashi 50 cikin 100 zai taimaka wajen rage wa iyaye da ɗalibai nauyin kuɗin karatu, tare da ƙarfafa matasa su rungumi fannonin kimiyya da fasaha da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ƙara da cewa jami’ar za ta ci gaba da faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi da ƙwarewa, musamman a fannoni masu tasowa da ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Arewa maso Gabas.

By ukarofi

Leave a Reply