Kotu ba ta soke zaɓukan fidda gwanin ADC ba, inji Atiku yayin da ya garzaya Kotun Ƙoli

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi watsi da iƙirarin cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar domin babban zaɓen 2027, yana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da ke ƙoƙarin ruɗar da ‘yan Nijeriya da raunana ɓangaren adawa.

Atiku, a wata takarda da Mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu ya fitar a ranar Litinin, ya yi kira ga mambobin ADC da magoya baya a sassan Nijeriya da su kwantar da hankali tare da cigaba da tsayuwa akan manufarsu, inda ya ce hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar bai shafi tikitin takarar shugaban ƙasa na ADC ba.

A cewarsa, hukuncin, wanda masu suka suka fassara, ya shafi manyan taruka da wa’adin kwamitocin zartarwa ne kaɗai, bai wa zaɓukan da ta gudanar bisa doka ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce kotuna suna da damar yin hukunci ne kaɗai akan abin da aka gabatar musu, ba waɗanda suke a wajen shari’a ba.

Don haka ne ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da ke sassan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu tare da cigaba da haɗa kansu domin tabbatar da cimma nasarori a zaɓen da ke tafe.

By Babaji

Leave a Reply