Kotu ta ɗaure Odita Janar shekara 5 a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu

Alƙalin Babbar Kotun Jihar Yobe, Mai Shari’a Muhammad Lawu Lawan, ya garƙame Odita Janar na Ma’aikatar Ƙananan Hukumomin Jihar Yobe, Alhaji Idris Yahaya, a gidan yari na tsawon shekara biyar, sakamakon samunsa da aikata almundahana da kuɗaɗen al’umma, ranar Litinin.

Kotun ta samu wanda ake zargin da laifin karkata akalar wasu kuɗaɗen da suka kai Naira miliyan 19,900,000 ba bisa ƙa’ida ba, wanda ofishin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na yankin, wanda yake a Maiduguri babban jihar Borno, ya gurfanar da shi.

Bayanai sun nuna Alh. Yahaya ya karɓi wannan kuɗin ne daga ofishin Ma’aikatar binciken kuɗaɗen Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Al’amurran Masarautu a jihar Yobe, waɗanda aka ware domin siyo mota ƙirar Toyota Corolla (2015 model) domin ayyukan ofis, inda ya karkatar da sashen kuɗin zuwa amfanin ƙashin kansa.

A ɗaya daga zargin ya ƙunshi: ”A matsayin ka na Yahaya Lawal Idris, Babban Mai Binciken Kuɗaɗe a Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi a Jihar Yobe, tsakanin ranar 20 zuwa 21 ga watan Mayun 2017 a Damaturu dake jihar Yobe, wanda wannan kotu ta gano ka karɓi Naira miliyan 19,900,000.00 ta amfani da asusunka mai lamba 1001480930 mai ɗauke da sunan: Alhaji Yahaya Idris a bankin ‘United Bank for Africa Plc’ (UBA) daga ma’ajiyar kuɗaɗen hukumar binciken kuɗin ƙananan hukumomi, mai lambar asusu: 5030030060 a bankin ‘Fidelity Bank Plc’ kuɗin da aka ware domin sayo sabuwar mota ƙirar Toyota Corolla 2015 Model, inda yin hakan rashin gaskiya ne kuma almundahana ne wanda za ka biya tarar naira miliyan 10,100,000.”

An fara gurfanar da mai laifin a gaban kotu tun ranar 9 ga watan Nuwamban 2022, inda ya musanta aikata laifukan, inda kotun ta ci gaba da bin diddigin shari’ar zuwa matakin ƙarshe. Wanda bisa ga wannan ne lauyan EFCC, Mukhtar Ali Ahmed ya gabatar da shaidu guda huɗu tare da kundi ɗauke da gamsassun bayanai kan zarge-zargen.

Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, Mai Shari’a Lawan ya bayyana wanda aka gabatar a gabansa da zargin aikata waɗannan laifukan, shaidu sun tabbatar da cewa ya aikata abubuwan da ake tuhumar sa. Wanda sakamakon haka, kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyar.

Bugu da ƙari, Mai Shari’a ya bayar da umurni ga mai laifin ya biya tarar naira miliyan 10,100,000 a biya gwamnatin jihar Yobe ta hannun hukumar EFCC ko ya fuskanci ƙarin shekara biyu gidan yari.