Shugaban APC ya amince akwai aibi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Litinin ya ce, zaɓen shugaban ƙasa da ’yan majalisun tarayya wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 ba cikakken mara naƙasu bane, domin an samu aibi.

Adamu ya faɗi haka ne a yayin da yake jawabi a wurin taron kwamitin gudanarwa na APC da shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima da zaɓaɓɓun mambobin majalisar tarayya.

Taron na sirri wanda bai fara gudana ba sai da misalin ƙarfe 2:48 na rana a ɗakin taro na Banquet House da ke Abuja.

Daga cikin manyan jiga-jigan da suka halarci taron har da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gabajabiamila, Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola, da sauransu.

Wannan taron na zuwa ne yayin da mambobin NWC suka fara kiran a sake fasalin jagorancin jam’iyyar kuma Adamu ya yi murabus domin saita tikitin Musulmi da Musulmi na gwamnati mai zuwa.

Da yake jawabi a wurin taron, Adamu ya taya dukkan zaɓaɓɓun ’yan siyasan murna, inda ya ce, sun cancanci haka bayan samun nasara a zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Shugaban APC, wanda ke fama da fafutukar kare kujerarsa, ya amince cewa zaɓen da ya gabata wanda ya ayyana su a matsayin masu nasara yana da naƙasu.

Adamu ya ce, “ina taya ku murna daga ƙasan zuciyata, na jinjina muku kuma ku ne sabon zubin Najeriya. Daga ranar 29 ga watan Mayu, duk wani zancen haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba zai dawo wuyanku.”

“Adalci ne mu amince cewa zaben 25 ga watan Fabrauru ba cikakke bane, dama bamu shirya gudanar da cikakken zaɓe ba, a tarihin duniya babu inda zabe ya gudana cikakke babu naƙasu.”

“Kamar sauran ƙasashen Demokuraɗiyya, mun shirya gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe, wannan kam mun cika. Ina alfahari mun cimma nasarar cika alƙawarin da shugaba Buhari ya yi wa mutane,” in ji shi.