Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta ba da umarnin karɓe Naira biliyan 1.37 na wucin gadi da ake zargin an karkatar da su daga asusun gwamnatin jihar Kaduna zuwa wani asusu na sirri.
Kuɗaɗen, wani ɓangare ne na kuɗaɗen da aka ware na aikin layin dogo da bai yi nasara ba a jihar Kaduna, ana zargin an karkatar da su ne a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai da ya mulki jihar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
Alƙalin kotun, H. Buhari, ya bayar da umarnin ƙwace kuɗaɗen ne a ranar 28 ga watan Faburairu, biyo bayan takardar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta gabatar, inda ta bankaɗo kuɗaɗen a cikin wani asusu na sirri.
Hukumar ta ce jami’an jihar Kaduna sun karkatar da kuɗaɗen ta hanyar wabi Kamfani Indo Kaduna MRTS Jɓ Nig. Ltd, tare da haɗin gwiwar wasu ‘yan kasuwa na ƙasar Indiya a cikin 2016.
Daga nan Alkalin ya ce a wallafa a shafukan jaridu duk wanda ya ke mamallakin wannan kuɗaɗe ya fito ya nuna na shi ne da shaidu da dalilan cewa kada a maida wa gwamnatin tarayya waɗannan kuɗaɗe.
Sai dai ba wannan ba kawai, gwamnatin Kaduna, na binciken wasu daga cikin kwamishinonin tsohon gwamnan jihar bisa zargin yin sama da faɗi da kuɗaɗen jihar a zamanin gwamnatin El-Rufai.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da wasu cikakkun hujjoji ba da ke nuna sun wawushe kuɗaɗen yayin da suka musanta duka zargin da ake musu.
