Kotu ta jaddada soke hukuncin dokar kamfanoni kan ikon hukumar CAC akan ƙungiyoyin addini da sauransu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta jaddada hukuncin Babbar Kotun Tarayya na soke hukunce-hukunce da dama na Dokar Kamfanoni da Makamantansu (CAMA), ta 2022, waɗanda suka bai wa Hukumar kula da Lamuran Rajistar Kasuwanci (CAC) iko akan lamuran haɗaka, ciki har da harkokin addini da wasu ƙungiyoyi.

A wani hukunci da alƙalai uku suka jagoranta, kotun ta ce sashen CAMA na 839, 842, 843, 844, 845, 846, 847 da 848 sun saɓa wa dokokin ƙasa na ‘yancin ɗaukar matsaya, addini, ƙungiya da haɗakar wasu jama’a da suka amince wa zama a inuwa guda. Haka kuma, kotun ta jaddada cewa, Emmanuel Ekpenyong, wanda lauya ne a ƙarƙashin Fred Young & Evans LP, yana da ‘yancin ya ƙalubalanci hukunce-hukuncen dokar bayan ya ce sun ci karo da ‘yancin da dokar ƙasa ta ba shi.

An fara wannan rikici ne kan dokokin CAMA tun a Agustan 2020 a lokacin da marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya mata hannu a dokance. Duk da cewa dokar ta gabatar da gyare-gyare masu yawa ga fannin harkokin haɗaka musamman ga hukunce-hukuncenta akan masallatai, coci-coci, gidauniyoyi, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauransu, lamarin da ya haifar da adawa daga ƙungiyoyin addini da na al’umma.

Ainihin abin da ya tayar da rikicin shi ne Sashe na 839 da ya bai wa CAC ikon dakatar da kwamitin amintattu da naɗa wasu jagorori a inda aka samu buƙatar haka, ciki har da zargin saɓa wa dokokin aiki da gudanarwa, almundahana ko inda aka samu halin shiga tsakani bisa la’akari da maslahar al’umma.

Wannan al’amari ya sa ƙungiyoyin suke fargabar hukunce-hukuncen ka iya bai wa gwamnati ikon gudanarwa sama da kima kan harkokin cikin gida na ƙungiyoyin. Akan haka ne ƙungiyoyin daban-daban suka riƙa kira da a yi wa dokar ta CAMA kwaskwarima ta yadda za a soke ko dakatar da wannan hukunci akan ‘yan kwamitin amintattu, ciki har da Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN).

A baya ne dai Babbar Kotun Tarayya ta soke hukunce-hukuncen bisa dogaro da Sashe na 38 da 40 na dokar ƙasa. Bayan haka ne lauyoyin tsagin CAC suka ɗaukaka ƙara, inda a nan ma ba su yi nasara ba.

By Babaji

Leave a Reply