Kotu ta kori ƙarar Gwamnatin Tarayya ta tuhumar bogi akan Adeyemin ‘hukumar bogi’

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yi watsi da tuhume-tuhume guda takwas da aka gabatar akan wanda aka yi zargin Darakta-Janar ne na hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi, wadda Gwamnatin Tarayya ta shigar.

Alƙalin ya yi watsi da ƙarar ne bayan gwamnatin ta gabatar da wata buƙata da kuma sharaɗin za a mayar da wanda ake zargin zuwa Babbar Kotun Abuja domin gudanar da sabon gurfanarwa.

A yayin zaman na ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, Lauyan Mai kare ɓangaren gwamnati tarayyar, Rotimi Oyedepo (SAN), ya gabata da ƙorafin neman a kawo ƙarshen tuhume-tuhumen.

Ya shaida wa alƙalin cewa Antoni Janar na Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, ya yi nazari akan takardar ƙarar Adeyemi da wanda Sufeto Janar na Ƙasa ya shigar, inda aka gano waɗansu kurakurai.

Daga dalilan, batun zargin takardun da Adeyemi ya yi aiki da su a matsayin na bogi wajen gudanar da harkokinsa, Babbar Kotun Abuja ce ya dace a kai wa ƙara a madadin Babbar Kotun Tarayya.

Daraktan Shari’o’in Al’umma na Tarayya (DPPF), ya ce an shigar da sabuwar ƙarar a Babbar Kotun ta FCT kuma za a gurfanar da Adeyemi a matsayin fara sabon shari’a. Akan haka ne ya buƙaci alƙalin kotun tarayyar da ya yi watsi da shari’ar kamar yadda doka ta buƙata.

Ganin cewa babu wani inkari daga Lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu, Mai Shari’a Umar ya kori ƙarar bisa tsarin kotu.

By Babaji

Leave a Reply