‘Yan takarar kujerar gwamna a Jihar Kebbi sun ayyana manufofinsu

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Ɗan takaran gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin jam’iyyar NDP, Ahmadu Zumaru, yace idan yaci zaɓe, zai fi bai wa harkokin ilmi da raya karkara da kuma tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, muhimmanci.

Ya fayyace haka ne a shirin musayar ra’ayi wanda ƙungiyar ‘yan jarida ta wakilan kafofin watsa labarai, watau (Correspondents Chapel Candidates Engagement Forum), ta Jihar Kebbi ta yi da shi a Birnin Kebbi.

Ɗan takaran na NDP yace zai yi jagorancin adalci, sannan kuma ya ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa.

Haka kuma, zai ɗora fifiko akan raya jihar Kebbi da bai wa ‘ya’yan talakawa musamman a yankunan karkara ingantaccen ilmi, sannan kuma ya ƙara kyautata jin daɗin malaman makarantu.

Dangane da ayyukan gona, Zarumai ya ce, zai ɓullo da dabaru da kuma bin hanyoyin da suka dace ya bunƙasa wadatar da ƙasa da abinci.

A nasa ɓangaren, ɗan takaran gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin jam’iyyar Accord Party, Muhammad Sani Abdullahi Bunza, cewa ya yi, zai ƙara nauyin aljihun ma’aikatan gwamnati su riƙa samun Naira 500,009 mafi ƙarancin albashi a kowane wata.

Ya yi furucin cewar abinda ake bai wa ma’aikata na albashi, abu ne ɗan cikin- cokali wanda baya wadatar da magidanta kula da iyalansu.

Ya ce zai dora fifiko wurin kyautata jin dadin ma’aikata domin su ne ginshiƙin raya ƙasa.

Dangane da tsaro, ya ce idan yaci zaɓe, zai haɗa ƙarfi da ƙarfe a tinkari faɗa da ta’addancin masu kai hare-hare da bindigogi , suna zaluntar al’umma, domin a magance lamarin.

Bunza ya kuma yi tsokaci akan aikin gona, ya ce zai ɓullo da dabarun aikin gona na zamani domin a haɓaka samar da isasshen abinci da sauran kayayyakin masarufi.

Ya ƙara da cewar zai kuma ɗora fifiko akan kiwon lafiya birni da karkara.

By ukarofi

Leave a Reply