Masu tallata Tinubu sun rabauta da motocin kamfe 32 a Bauchi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU

Ƙungiyar tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai suna PBAT Door-to-Door, reshen Jihar Bauchi, ta rabawa mambobinta motoci 32 domin ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

Jagoran ƙungiyar na ƙasa, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ne ya bayar da motocin. An gudanar da rabon ne ta hannun wakilinsa, Kestin Pondi.

An raba motocin ne domin sauƙaƙa wa mambobin ƙungiyar gudanar da ayyukansu a ƙananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi, kamar yadda jami’in kula da ƙungiyar a matakin jiha, Muhammad Auwal Abubakar, ya bayyana.

Daga cikin waɗanda suka halarci bikin rabon motocin akwai ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Muhammad Abubakar Bala Maijama’a, da sauran shugabannin jam’iyyar a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply