Alƙalin alƙalai ta rantsar da sababbin manyan lauyoyi 68 masu darajar SAN

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere Ekun ta rantsar manyan lauyoyi a muƙamin Senior Advocate of Nigeria (SAN) su guda 68 a taron Masana Shari’a na Shekara (LY) na 2026/2027.

Gidan talabijin na ƙasa (NTA) ne ya sanar da wannan ci-gaba a sahihin shafinsa na X a ranar Litinin, inda ya yaɗa bidiyo da hotunan wajen taron.

Hakan ya biyo bayan amincewar Kwamitin Walwalar Masana Shari’a (LPPC) kusan watanni uku da suka gabata. Kwamitin ya amince da lauyoyi 68 ɗin ne matsayin a yayin zamansa na 174, wanda Kekere Ekun ta jagoranta.

A cewar wata sanarwa da Babban Rajistiran Kotun Ƙoli da Sakataren LPPC, Kabir Eniola suka fitar, sababbin SANs ɗin sun haɗa da manyan lauyoyi 67 da farfesan ilimi guda, Farfesa Nnamdi Onyeka Obiaraeri.

Muƙamin SAN ɗaya ne daga cikin darajojin ƙwarewar matakin ƙoli a fannin shari’ar Nijeriya. Ana bayar da shi ne ga masana shari’ar da suka nuna ƙwarewa yayin gudanar da lamuran kotu ko bayar da gagarumar gudunmawa ga ci-gaban shari’a a fannin ilimi, lamarin da ya sa aka samu farfesa acikinsu.

By Babaji

Leave a Reply