Daga UMAR GARBA a Katsina
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba wa hakiman masarautar Katsina kyautar Naira miliyan 50, inda kowannensu zai samu Naira miliyan ɗaya.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ne ya bayyana hakan tare da cewa kowane magajin gari a ƙarƙashin hakiman zai samu kyautar Naira 100,000.
Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya sanar da hakan ne a ranar Asabar fadar maimartaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir, lokacin da aka gudanar da ɗaurin auren ’ya’yan sarkin guda uku, maza biyu da mace ɗaya.
Masari, wanda ya wakilci tawagar shugaban ƙasa a wajen bikin, ya ce Tinubu na taya Sarkin Katsina, Mai Martaba Dakta Abdulmumini Kabir, murna tare da yi masa fatan alheri
Ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da yi wa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya da kawo ƙarshen matsalolin da ake fuskanta.
Ministan gidaje, Dakta Muttaƙa Rabe Darma, da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, na daga cikin manyan mutanen da suka halarci bikin tare da Masari.
Sai dai ba a ga wani daga cikin manyan jami’an gwamnatin Jihar Katsina a wajen taron ba, lamarin da ya sake jawo tambayoyi kan rahotannin da ke cewa akwai rashin jituwa tsakanin Gwamna Dikko Raɗɗa da Ibrahim Masari.
