2027: Jamilu Gwamna ya ɗauki mata a matsayin ginshiƙin ci gaban Gombe — Shawai

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI r, Gombe

Mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, Ibrahim Sani Shawai, ya ce inganta rayuwar matasa da mata na daga cikin manyan manufofin ɗan takarar a zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Ya bayyana cewa ɗan takarar ya yi imanin cewa ci gaba mai ɗorewa ba ya taƙaita ga gina hanyoyi da gadoji kawai, sai an kuma inganta rayuwar jama’a tare da samar musu da damar cin gajiyar tattalin arziki.

A cewarsa, matasa da mata ya kamata su kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar jihar, maimakon kasancewa masu jiran manufofin gwamnati kawai.

Shawai ya ce ƙwarewar Dakta Gwamna a harkokin kamfanoni masu zaman kansu da gudummawar da ya bayar wajen tallafa wa ilimi, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi sun taimaka wajen tsara hangen nesansa kan shugabanci.

“Gina hanyoyi da gadoji yana da muhimmanci, amma gina ɗan Adam shi ne abin da ke tabbatar da ɗorewar ci gaba. Idan aka inganta ilimi, kiwon lafiya da ƙwarewar jama’a, za a samar da ginshiƙin tattalin arziki mai ƙarfi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Dakta Gwamna na goyon bayan ci gaba da kyawawan manufofin da aka aiwatar a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da ɓullo da sabbin dabaru domin magance ƙalubalen da har yanzu suke fuskantar al’ummar jihar.

Shawai ya bayyana zaɓen 2027 a matsayin wata dama ga al’ummar Gombe ta zaɓar shugabancin da zai ba da fifiko ga bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da faɗaɗa damar samun ci gaba.

Ya jaddada cewa hangen nesan Dakta Jamilu Gwamna shi ne gina Gombe inda matasa za su samu damar cimma burinsu, mata su taka rawa a tattalin arziki, sannan kowane ɗan ƙasa ya samu damar cin moriyar ci gaban jihar.

By ukarofi

Leave a Reply