Kotu ta sake tsare Abba Kyari da wasu mutane shida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Emeka Nwite wanda ke sauraren ƙara da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta shigar tana tuhumar babban jami’in ɗan sanda Abba Kyari da wasu mutum shida ta ƙi amincewa da buƙatar da lauyoyinsa suka miƙa mata na a bayar da belinsa.

Sai dai kotun ta ce za ta saurari buƙatar a zamanta na gaba.

Lauyan Abba Kyari, Kanu Agabi ya shaida wa manema labarai a gaban kotun cewa kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar Litinin 14 ga watan Maris domin sake duba batun belin.

Amma ya qi cewa komai game da abubuwan da suka wakana cikin kotun, ciki har da miƙa wuyan da wasu mutum biyu cikin mutum shidan da ake tuhuma da aikata laifukan suka yi.