An baza jami’an tsaro a sakatariyar APC bayan tsige Buni a matsayin shugaban jam’iyya

Daga BASHIR ISAH

An baza jami’an tsaro a babban ofishin APC da ke Abuja biyo bayan tsige Gwamna Maimala Buni da Buhari ya yi a matsayin shugaban kwamitin riƙo na ƙasa na jam’iyyar.

Tun da misalin ƙarfe takwas na safiyar Litinin ɗin nan aka girke jami’an tsaro a ciki da wajen sakatariyar da nufin tabbatar da bin doka da oda.

Duk da tsige Buni da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a matsayin shugaban riƙo na APC, Gwamna Buni ya ci gaba da iƙirarin cewa har yanzu shi ne ke riƙe da jam’iyyar, tare da bayyana labarin tsige shi a matsayin rahoton ƙarya.

Buni ya yi iƙirarin nasa ne cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Litinin wadda sakatarensa na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce, “Hankalinmu ya kai kan wani rahoto game da samun sauyin shugabanci a jam’iyyar APC.

“Wannan labari dai ƙarya ne wanda bai kamata a kula shi ba.

“APC jam’iyyar siyasa ce mai gudana kan dokoki. Ba haka kawai ake sanar da sauyin shugabancin ba ta hanyar mabaton suna da kuma yaɗawa a labarai.

“Muna kira ga magoya bayanmu da ma al’umma baki ɗaya a kan kowa ya kwantar da hankali tare kuma da ci gaba da bai wa APC ƙarƙashin jagorancin Gwamna Maimala Buni goyon bayan wajen ganin ya gudanar da babban taron APC cikin nasara.”

Da alama dai tun a ranar Lahadi da daddare Buhari ya zartar da wannan matakin kafin ya keta hazo zuwa London don duba lafiyarsa.