Kotu ta tabbatar da Aminu Ado a matsayin sarkin Kano

Wata babbar kotu a Kano ta jingine dokar da ta kawo naɗin Sarki Sanusi na II. Mai sharia Abdullahi Liman shine ya tabbatar da haka a yayin zaman da akai a kotun yau.

Mai shari’ar ya kuma ba masu ƙara cewa kowa ya zauna matsayin sa har sai kotu ta gama zaman sauraren ƙarar baki ɗaya. Bayan haka ne ya miƙa cigaba da sauraren shari’ar ga babbar kotu ta uku.