Kotu ta tsare Alhassan Doguwa a kurkuku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kotun Majastare a Kano ta tisa ƙeyar Shugaban Masu Rinjaya a Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, zuwa gidan yari kafin lokacin da za a ba da belinsa.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mai kare kansa, Alhassan Doguwa, na fuskantar tuhuma ne kan laifuka da dama da suka haɗa da kisan kai, haɗin baki, mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba da tada fitina a tsakanin al’umma.

Alƙalin kotun, Ibrahim Mansur Yola, shi ne ya ba da umarnin tsare Doguwa a kurkuku zuwa 7 ga Maris inda za a saurari neman belinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *