NPC ta cafke mai yi mata sojan gona a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) reshen Jihar Kano ta nesanta kanta da bayanan dake yawo na karɓar 5000 don tabbatar da sunan wanda suka cike aikin ƙidaya na wucin-gadi a jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar a jihar Kano, Hajiya Jamila Abdulkadir, wadda aka raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ce, bisa bayanan da ta samu ta sa jami’an tsaro bincikar lamarin.

Kalika, sanarwa ta ce waɗannan masu karɓar kuɗin da sunan za su tabbatar ma wanda ya cike gurbin aikin wucin-gadi na ƙidaya ba su da alaƙa da su, kuma ba ma’aikatan su ba ne.

Sanarwar ta tabbatar da nasarar damƙe wani daga cikin masu yin wannan aika-aika a ƙaramar hukumar Wudil tare da damƙa shi ga ‘yan sanda don gudanar da bincike.

Da wannan ne hukumar ta ƙara jan hankalin al’umma da cewa su ƙaurace wa duk wasu dake karɓar kuɗi don tabbatar da bayanansu kan batun ƙidaya a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *