Kotu ta tsige sanatan Adamawa daga kujerarsa

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja, ta tsige Sanata Ishaku Abbo mai wakiltar Adamawa ta Arewa daga kujerarsa.

Kotu ta yanke hukunci kan shari’ar ne a ranar Litinin inda ta karɓe kujerar Sanatan Adamawa ta Arewa daga hannu Abbo tare da bayyana ɗan takarar jam’iyyar PDP, Amos Yohanna a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Da yake ysokaci jim kaɗan bayan hukuncin da kotun ta yanke, Abbo ya yi alƙawarin zai yi sanarwa a shafinsa na facebook.

Daga nan ya ui kira ga jama’ar mazaɓarsa kan cewa kowa ya kwantar da hankalinsa.