Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun Tarayya da ke zama a Legas ta umarci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi guda 71 da su sanya takunkumin fitar da kuɗi daga wasu asusu da ake zargin an yi amfani da su wajen adana wani kaso na Naira biliyan 1.34 da aka karkatar ba bisa ƙa’ida ba daga asusun wasu kwastomomin Bankin Access, ta hanyar manhajar bankin ta intanet mai suna Access SME App.
Mai shari’a Akintayo Aluko ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin, bayan lauyan Bankin Access, Ifeoma E. Enyinnaya, ta shigar da buƙatar gaggawa a gaban kotun ba tare da sanar da ɓangaren da ake ƙara ba.
Bankin ya nemi kotun ta sanya wa asusun da ake zargin sun amfana da kuɗaɗen takunkumin Post-No-Debit (PND), wato hana fitar da kuɗi daga asusun, tare da sanya ido kan Lambobin Tantance Banki (BVN) da ke da alaƙa da waɗanda suka karɓi kuɗaɗen.
A cikin takardar ƙarar da aka shigar ranar 13 ga Agusta, Bankin Access ya ce ya gano faruwar damfarar ne ranar 12 ga Agusta 2026, inda aka yi amfani da manhajar bankin ta intanet wajen karkatar da kuɗaɗen wasu kwastomomi.
Bankin ya bayyana cewa binciken cikin gida da ya gudanar ya gano cewa an fitar da jimillar N1,340,425,393, wato Naira biliyan ɗaya da miliyan 340 da dubu 425 da ɗari 393, daga asusun kwastomominsa ba tare da izini ba.
An ce an tura kuɗaɗen zuwa wasu asusu da ke Bankin Access da kuma wasu cibiyoyin hada-hadar kuɗi 71. A cewar takardun da bankin ya gabatar wa kotu, an gano lamarin ne bayan ma’aikatan bankin sun koma aiki a ranar 12 ga Agusta, inda suka lura da wata damfara da aka aiwatar ta hanyar Access SME App.
Saboda haka, Access Bank ya nemi kotun ta bayar da umarni guda huɗu, ciki har da hana fitar da kuɗi daga asusun da ake zargin sun karɓi kuɗaɗen da aka karkatar. Bankin ya kuma nemi waɗannan cibiyoyin kuɗi su gabatar da bayanan adadin kuɗin da suka samu damar tsarewa daga cikin kuɗaɗen da aka karkatar.
Bankin Access ya kuma nemi a sanya BVN na asusun da ake zargin sun amfana da kuɗaɗen cikin jerin waɗanda za a sa ido a kansu, har sai an gano ko an dawo da dukkan kuɗin da aka karkatar, gwargwadon abin da kowane mai amfana ya karɓa.
Bugu da ƙari, bankin ya nemi kotun ta umarci cibiyoyin kuɗin da su mayar da duk kuɗin da aka samu damar karbewa zuwa wani asusun Bakin Access mai lamba 0703060877. Sai dai yayin yanke hukunci kan buƙatar, Mai shari’a Aluko ya amince da buƙatu uku na farko.
Hakan ya sa kotun ta bayar da umarnin:
Hana fitar da kuɗi daga asusun da abin ya shafa; Tilasta wa cibiyoyin kuɗin da ake ƙara su bayyana adadin kuɗin da aka samu damar tsarewa; da sanya lambobib BVN da abin ya shafa cikin jerin waɗanda za a sa ido a kansu.
Sai dai kotun ta ƙi amincewa da buƙata ta huɗu, wadda ta nemi a mayar da kuɗaɗen da aka samu damar karɓewa zuwa asusun Bankin Access. Mai shari’a Aluko ya ce bayar da irin wannan umarni a wannan mataki na iya zama tamkar hukuncin ƙarshe kan batun. Daga bisani, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa 31 ga Agusta 2026.
Cibiyoyin da aka ambata a cikin ƙarar sun haɗa da Accion Microfinance Bank, Addosser Microfinance Bank, Alternative Bank, Alpha Morgan Bank, Ecobank, Fidelity Bank, First Bank, First City Monument Bank (FCMB), Globus Bank, Guaranty Trust Bank (GTBank), Jaiz Bank, Keystone Bank, Kuda, LAPO Microfinance Bank, Moniepoint, Opay, PalmPay, Polaris Bank, Providus, Stanbic IBTC, Sterling Bank, Union Bank, United Bank for Africa (UBA), Wema Bank da Zenith Bank, da sauran bankuna da cibiyoyin kuɗi.
