Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jaddada ɗaurin da aka yi wa Faruk Lawan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara a jiya Alhamis ta rage shekarun da a ka yanke wa tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Faruk Lawan a  gidan yari zuwa biyar.

A watan Yuni, 2021 ne wata Babbar Kotun Abuja ta kama Lawan da laifuka uku da su ka haɗa da neman rashawa, yarda da karɓar rashawa sannan da ga ƙarshe ya karɓi rashawa ta dala 500,000 da ga wani ɗan kasuwa, Femi Otedola.

Da ga bisani ne dai kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Angela Otaluka ta yanke wa Lawan hukuncin shekara 7 a kan laifi ɗaya, ya kuma ɗaure shi shekaru 7 a laifi na biyu sai kuma ya ɗaure shi shekara 5 a laifi na uku.

Amma kuma a wani hukunci na bai-ɗaya a jiya Alhamis, wani kwamitin mutane uku na kotun ɗaukaka ƙarar, ƙarƙashin jagorancin shugabar kotun, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ya yi watsi da hukuncin Lawan kan laifi na daya da na biyu.

Kwamitin ya nuna cewa mai ƙara ya gaza fansar da kotu cewa Lawan ya nema da kuma yarda da karɓar rashawa ta dala miliyan 3 da ga Otedola.

Kotun ta tabbatar da cewa mai ƙarar ya iya tabbatar da laifi na uku, wanda yake da nasaba da karɓar rashawar dala 500,000.
Da ga nan ne sai kotun ta wanke Lawan da ga zargin laifi na ɗaya da na biyu, wanda a ka yanke masa shekaru 7 ko wanne, amma kuma ta tabbatar da hukuncin laifi na uku, wanda a ka yanke masa shekaru biyar.