Wata kotu a Amurka ta bayar da umarni ga hukumar FBI da hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta DEA su fitar da bayanan bincike da suka shafi Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, dangane da zargin hannu cikin safarar miyagun ƙwayoyi a shekarun 1990s. Mai shari’a Beryl Howell ce ta yanke wannan hukunci, biyo bayan ƙarar da wani ɗan Amurka mai suna Aaron Greenspan ya shigar yana neman sake duba hukuncin baya. Greenspan ya nemi bayanan ta hanyar dokar FOIA (Freedom of Information Act), amma an hana shi samun bayanan a baya bisa dalilin kare sirri da tsaro.
A cikin bayanan kotun, akwai wata sheda da ke nuna cewa Tinubu na da alaƙa da wasu mutane da ake zargi da harkar safarar heroin a birnin Chicago. Bayanai daga wata shaida ta Kevin Moss, wani jami’in bincike na hukumar IRS a wancan lokacin, sun bayyana cewa akwai yiyuwar kuɗin da Tinubu ya ajiye a wasu asusun banki sun fito ne daga safarar miyagun ƙwayoyi. Kotun ta bayyana cewa, duk da koke-koken da Tinubu ya gabatar na kare sirrin sa da bayanan haraji, buƙatar jama’a ta sanin gaskiyar abin da ke ciki ya fi ƙarfin sirri.
Duk da cewa CIA ta ci gaba da kare matsayinta na rashin faɗin ko tana da bayanan ko a’a, kotun ta umurci sauran hukumomin da aka shigar da ƙara su fitar da rahoto kan halin da ake ciki kafin 2 ga Mayu, 2025. Wannan hukunci na iya haifar da fitar da muhimman takardu da suka jima suna janyo cece-kuce a siyasar Najeriya, musamman bayan zargin da aka daɗe ana yi wa Tinubu tun kafin zaɓensa a 2023.
