Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta bayar da shawarar ƙarin kashi biyar cikin 100 na ƙarin kuɗin kiran waya, inda ta yi watsi da ƙarin kashi 50 cikin 100 da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta amince da shi.
Mai magana da yawun NLC, Benson Upah, ya bayyana hakan a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talbijin na Channels a ranar Alhamis.
“Suna ci gaba da lalata mana al’amura ta hanyar harajin wauta. Koda wasu mutane za su iya biya wasu ba za su iya biya ba. Dole a dakatar da wannan ƙarin kuɗi na rashin hankali. Idan har ya zama wajibi a ƙara, to sai dai a ƙara kashi biyar, idan aka yi la’akari da gaskiyar halin da muke ciki.
“Amma yanzu a ce kashi 50, ba zai yi aiki ba. Ina talakawan Nijeriya za sa sa kansu bayan ƙarin kuɗin wutar lantarki?”
A cewarsa, babu gudu babu ja da baya kan zanga-zangar da ta shirya yi a faɗin aasar a ranar Talata 4 ga watan Fabrairun 2025, domin kawar da rashin jin daɗin ƙumhiyar dangane da ƙarin kuɗin kira waya, saƙon tes da data da aka yi kwanan nan.
“Masu sana’a suna nishi, masu matsakaicin matsayi suna nishi. Talakawan Nijeriya da ke kan tituna ba su ma iya kunna fitulun ɗakunansu. Lokacin da haraji ya yi ƙasa, mutane da yawa fiye da lokacin da kuke da haraji mai yawa,” inji shi.
Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF a ko da yaushe suna ba da shawarar cire tallafin makamashi da kuma shawagi na Naira, suna masu cewa rashin aiwatar da manufofin tattalin arziki guda biyu ya jefa Nijeriya cikin mawuyacin hali na hauhawar farashin kayayyaki.
