Ku lura da tarbiyyar ‘ya’yanku, kiran Hajiya Salifat Sule ga iyaye

Daga BASHIR ISAH

Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa, Hajiya Salifat Sule, ta jaddada buƙatar da ke akwai iyaye su zamo masu saka ido matuƙa a kan tarbiyyar ‘ya’yansu don amfnin al’umma baki ɗaya.

Salifat ta yi wannan kira ne a jawabin da ta yi wa alhazan jihar sa’ilin da ta kai musu ziyara ranar Alhamis a Mina a ƙasar Saudiyya.

Ta ce, aikin lura da tarbiyyar ‘ya’ya bai kamata ya a bar shi a hannun iyaye mata kaɗai ba, don haka ta buƙaci iyaye maza da su kasance masu mara wa matan baya yadda ya kamata a fagen bai wa yara tarbiyya ta yadda za a reni ‘ya’ya ababen alfahari.

Baya ga yaba wa Hukumar Alhazan Jihar Nasarawa dangane da namijin ƙoƙarin da ta yi wajen yi wa alhazan jihar hidima yadda ya kamata daga farko zuwa kammala aikin Hajji, Hajiya Salifat Sule ta kuma yaba wa alhazan bisa addu’o’in da suka zazzaga wa jihar a ranar Arfa.

A nasa ɓangaren, Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar, Malam Idris Ahmad Almakura, ya shaida wa alhazan cewar, Gwamna Abdullahi Sule ya amince da a bai wa kowannensu Riyal 100, kwatankwacin Naira 20,000, a matsayin ‘Goron Sallah’, lamarin da ya faranta wa alhazan rai matuƙa.

Majiyarmu ta ce Alƙalin-Alƙalan Jihar Nasarawa, Mai Shari’a Aisha Bashir Aliyu, na daga cikin waɗanda suka mara wa Hajiya Salifat baya yayin ziyarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *