Sharhin littafin ‘GAWA da RAI’

Daga BAMAI A. DABUWA KKM

Sunan Littafi: Gawa da Rai.
Sunan Marubuci: Yusuf Yahaya Gumel.
Shekarar Bugu: 2022.
ISBN: Babu.
Bugu: AGK Graphics Kurna.
Yanayi: Ba A Fayyace ba.
Jigo: Soyayya.
Salo: Cikin Fage.
Mai Sharhi: Bamai A. Dabuwa Kkm.
Lambar Wayar Mai Sharhi: 07037852514.
Email: [email protected]

GABATARWA/TSOKACI.

Littafin Gawa da Rai, labari ne na wani matashi (Anas), mai fama da larurar ‘Cotard Delusion’. Wata kalar cuta ce, da idan ta kama mutum sai kawai ya gamsu a ransa cewa shi matacce ne ko kuma dai ya rasa wani sashe na jikinsa, alhalin ba hakan ba ne. Tauraron ya kamu da soyayyar wata yarinya (Laila). ‘Yar gidan wani hamshaƙin mai kuɗi, wanda ya sallama ruhin ‘ya’yansa ga matsafa domin cimma muradin zuciyarsa na Duniya. Shigowar Anas rayuwar ‘yarsa (duk da cewar a makare ne), ya yi sanadiyyar tonon asirinsa. Daga ƙarshe, tauraron ya warke, sai dai saƙon da ya ci karo da shi ne zai sa mai karatu ya ji a ransa cewa akwai sauran rina a kaba.

ABUBUWAN BURGEWA.

Mutane dayawa suna cewa, babu wani abu mai saurin kintata ko fahimta irin akasarin littatafan Hausa da shirye-shiryen su na fim. Ta yadda wasun, farkon labari kawai za su karanta su fahimci inda ya dosa. Saɓanin akasari, an yi ƙoƙari ainun wajen ɓadda ƙafa a wannan littafin. Wani zai ɗauka an gina wannan labarin a kan fatalwa ne, alhalin ba hakan ba ne. Dole ne mu jinjinawa basirar marubucin sosai. An yi ƙoƙari ainun wajen kiyaye ƙa’idojin rubutu.

KUSKURE.

Ba abu ba ne mai sauƙi kawo duk wasu matsala ko kuskure da aka samu a wannan littafin ba, hasalima idan aka ce kowane kuskure da ke cikin za a kawo to kuwa girma da faɗin abin da aka kaucewa ɗin a rubuce sai ya linka girman littafin, idan za a fayyace su dalla-dalla. Salon da aka yi amfani da shi ba mai armashi ba ne. Akwai ƙarancin balaga da karin magana a labarin (ba lallai ka samu karin magana sama da huɗu ba a duk littafin). An yi ƙoƙarin cika littafin da labarai marasa alaƙa ko kan gado. Ga kaɗan daga cikin abubuwan da aka kuskure ɗin.

  1. Sunan Littafi:

A tsari da jadawalin samarwa da rubuta sunan littafi ko taken wani labari ko saƙo (title), musamman wanda muke ara daga Turanci ko kuma na ce wanda muka yi tarayya wajen tsarawa. Kamar su APA, AMA da saura. Mun sani kuma mun fahimta cewa, kuskure ne fara rubuta wasu kalmomin da babban baqi. Kalmar ‘da’ na jikin sunan labarin ba ta daga cikin wace ya kamata a fara da babban baƙi. Ke nan sunan littafin kamata ya yi ya kasance haka Gawa da Rai maimakon Gawa Da Rai kamar yadda marubucin ko masu bugawa suka buga.

  1. Kuskuren ƙa’idojin Rubutu.

A wurare masu yawa, marubucin bai kiyaye wasu tsari da yadda ya kamata a rubuta wasu kalmomin ba. Misali:
~fahimtarsa maimakon fahimtar sa (4).
~Cikin su maimakon cikinsu (4).
~kaya na maimakon kayana (4).
Wasu daga cikin kalmomin su ne kamar haka: duniya, kenan, gareni,

2.1. Sanyawa da Rashin Sanya Alamomi a Inda Suka Dace.

An samu saɓani sosai wajen sanya alama a wasu wuraren da ba su dace ba. Wasun kuma ba a sanya su a wuraren da ya kamata a ce an saka su ba. A taƙaice ma, a kaso 70 cikin ɗari na duk inda aka saka waƙafi ko aya ba su dace da wurin ba. Misali:
“Na yi kokawar buɗe idanuna, kur na zuba su a ɗakina nake tabbas, na nazarci…” (4).
Akwai buqatar sanya alamar waƙafi ko aya a gaban kalmar su, sannan kuma aya a gaban kalmar tabbas. Kamar haka:
Na yi kokawar buɗe idanuna, ƙur na zuba su, a ɗakina nake tabbas.

  1. Maimaita Saƙo/Ma’ana.

Ga wanda suka gaza rabe yadda ake amfani da salo tafiyar kura ko je ka ka dawo a labari, yana nufin kamar ana tsaka da al’amari a wannan shekarar da ake ciki 2023, sai kuma a bari a koma baya kamar 1994. A fim shi ne kamar flashback. Haɗaɗɗen salo ne kuma ya halatta a rubutu. Sai dai ya sava sosai kuma da dawurwurwa ko dibi-dibitu a wuri guda. Wato maimaita ma’ana ko saƙo zunubi ne a rubutu wanda ke haifar da gundura ko raina fahimtar mai karatu. Misali: Ya zo kamar haka a shafi na 4, sakin layi na farko kamar haka:

“Na yi kokawar buɗe idanuna, kur na zuba su a ɗakina nake tabbas,…”(4).
Sai kuma a gaba, shafi na 4, sakin layi na biyu kamar haka:
“Na cigaba da kai kallon ga gadon da bake kwance tabbas a ƙarshe na samu gamsuwa a ɗakina nake,…”(4).
Abin da ya zo a sakin layi na farkone aka maimaita a sakin layi na biyu. Wanda babu bukatar hakan.
Har’ilayau, an maimaita makamancin wannan kuskure a wurare masu yawa. Duba shafi na 16, sakin layin ƙarshe.
“,…sai ga likitan a gaba yana sanye da shigar likitoci dogo ne sosai kuma siriri ne, ba abu ba ne mai sauki ka iya hasashen shekarunsa ta hanyar la’akari da yanayin fasalin jikinsa, sakamakon ɗan ƙaramin jiki da yake da, babu kuma nama a tare da jikin.”(16).

Ba wai yadda marubucin ya cika amfani da kalmar ‘ne’ da kuma ‘jiki’, ko yadda ya kawo kalmar ‘yanayi’ da ‘fasali’ a wuri guda ba ne kawai kuskure face yadda ya bayyana likitan a matsayin siriri da ya yi tun farko amma duk da haka ya dawo yana cewa marar nama. Da ma kam wane siririn mutum ne mai nama?

  1. Kuskuren Azancin Magana Daidai da Yanayi/Kamala/Tsari/Ɗabi’a.

4.1. Professor Wole Soyinka ya tava faɗa da Turanci, kamar haka: ‘To everything it’s place.’ A sauƙaƙe, kana da Hausa abin da ake nufi shi ne ‘Wa Komai Gunsa.’ Ma’ana; kuskure ne kuma ya sava kamala a raka gawa da mutum, amma ya vige da cin goro ko aswaki a maƙabartar. Ya zo kamar haka a shafi na 4, sakin layi na huɗu kamar haka:
“Wayyo rayuwar kenan shi kenan Anas ya mutu duniya ke nan ba matabbata ba ce. Na ji yayana yana furta wasu kalamai cike da kuka da gunji”(4).
Wannan maganar sam ba ta dace wanda ya rasa ƙaninsa na jini kuma a lokacin da ya mutu ba. Ya fi kamata da jawabin maƙota ko wasu masu jaje na gefe.

4.2. “”Wane Anas ɗin?”

Na samu kaina da tambaya da ƙarfi amma abin mamaki ko na kira shi da takaici babu wanda ya kula ni, ballantana na sa ran ji daga gare su,…”(4).

An kuskure wa azanci a wannan jimlar. Dalili: wanda ka kira bai amsa ba, za ka sa a ranka bai ji ka ba ne. Ke nan ba abin mamaki ba ne.

4.3. A yadda bincike da yadda mutane duka fi gamsuwa da shi dangane da fatalwa, shi ne ba su iya kamawa ko taɓa jikin mutum. Sai dai su ratsa su wuce ko a ratsa su. Ya zo kamar haka a shafi na 7 sakin layi na huɗu:
“Sauri na ƙara sosai na riske shi na kai hannu na kama hannunsa ina kokarin ya gan ni.”(7).

  1. Kuskuren Haifar da Rashin Tabbas da Ruɗu.

“Wayyo rayuwar kenan shi kenan Anas ya mutu duniya ke nan ba matabbata ba ce. Na ji yayana yana furta wasu kalamai cike da kuka da gunji”(4).

Fadin cewa na ji yayana yana furta wasu kalamai cike da kuka da gunji, kuskure ne domin an riƙa an kawo kalaman da ya furta ɗin. Kalmar wasu da aka shigar a wajen za ta sa mai karatu ya ɗauka akwai wasu kalaman kuma, sannan babu buƙatar kawo kalaman nasa, domin kalmar wasu na nufin an sakaye su ne.

  1. Hausar Baka.

~Ballantana.
~Sulɓulewa.
~Sulge.

  1. Kufcewar Salo.

Mafi girman kuskure da marubucin ya tafka a labarin, wanda ya lalata nagarta da cikakken saƙon da marubucin ke son isarwa a kan tauraron. Kana ya raunana tare da bayyana ƙarancin bincike ko cikakkiyar fahimtar abin da saƙo ko larurar da ake son magana a kai bayan mun yi uzuri ga yadda ya rubuta sunan jinyar kamar haka “cotard delusio”(24) a maimakon ‘cotard delusion’. Shi ne yadda a littafin shafi na 24 zuwa 27, likitan ya bayyanawa tauraron da iyayensa cewa ya kamu da larurar ‘cotard delusion’.

Sai dai, abin da yake na zahiri wanda bincike ya samar na wannan jinya, kamar yadda ya a zo a bayanin likitan shi ne; mutum ya gamsu a ransa cewa shi matacce ne ko kuma ya rasa wani sashe na jikinsa kodakuwa da ransa ko bai rasa koman ba. Yadda marubucin ya bayyana jinyar a aikace ta hanyar tauraron ya ci karo da yadda jinyar take a zahiri. Domin kuwa tauraron (wanda ke fama da jinyar), bai yarda ya mutun ba, hasalima shi ne yake ƙoƙarin fargar da iyayensa cewa bai mutu ba.

A sauƙaƙee, yadda marubucin ya bayyana alamomin jinyar a aikace a jikin tauraron sun sava da bayanin da ya kawo game da jinyar ta bakin likita (duba shafi na 4 zuwa 27). Wanda kuma hakan ya haifar da wata matsalar ta cewa likitan bai san aikinsa ba, domin ya ɗora marar lafiya a kan jinyar da ba ita ke damun sa ba. Ke nan ta kowace fuska an samu kufcewar salo. Ga liƙau nan domin samun ƙarin haske dangane da jinyar https://www.ncbi.nlm.nih.gov/pmc/articles/PMC2695744/

Sannna da za a faɗaɗa binciken abin da ke haifar da wannan jinya, za ka fahimta cewa a labarin babu inda tauraron ya haɗu da silar jinyar, sannan haka kawai ya warke ba tare da wani magani ba.

7.1. Har’ilayau, a farkon labarin wanda ya fara a shafi na 4 zuwa 6. Ya bayyana yadda tauraron ya yi ta ƙoƙarin fargar da iyayensa cewa yana da rai (domin bai gamsu shi fatalwa ba ne sannan) kamar yadda ya yi ta ihu, magana da sauran domin a ji shi amma a banza. Kawai sai kuma a shafi na 6, sakin layi na ƙarshe ya zo kamar haka:

“,…hannu na ɗaga amma kuma ya gaza gani har ma ya gane cewa rayayyu biyu ne,…”(6).
Cewa ya gaza gani kuskure ne a jimlar domin har sannan shi bai fahimci ba sa ji da ganinsa ba.

TAMBAYOYI.

  1. Me ya sa a sakin layin ƙarshe, shafi na 9, marubucin ya rubuta kamar haka: Gawa da rai! Me ya sa kalmar gawa ta fara da babban baƙi? Me ya kawo alamar motsin rai wajen?
  2. Fatalwa na iya jin ciwo?
  3. A wane gari aka gina labarin?

ƘAƘRAREWA.

Daga ƙarshe, dole ne mu jinjinawa marubucin wannan littafi bisa sabon ilmin da ya kawo mana. Ban tava sanin akwai yanayin da mutum zai shiga ba ya riqa yi wa kansa kallon matacce ba ko kuma ya yarda cewa ba shi da ido ba, alhalin yana gani. Astagfirullah! Na taɓa gani a wani shiri da Ibro yake kuka wai ya rasa cikinsa. Na ɗauka illar wiwi ne (Kodayake nan ɗin wiwin ce).

Abin da nake nufi shi ne bayan shaye-shaye ban san kuma mutum na iya shiga yanayin ba sai a wannan littafin. Hakan ne ma ya sa ni faɗaɗa bincike a kai. Ina godiya sosai da wannan ilmi. Sannan yana da kyau idan muka fahimta cewa kuskure wa jinyar da muka yi magana a sama ba a kan bayanin ta da likita ya kawo ba ne, muna nufin yadda marubucin ya bayyana ta a aikace ne a jikin tauraron kuskure.

Allah ya ƙara basira da ilmi mai albarka.

Domin gyara ko shawara, za a iya tuntuɓa ta a:
[email protected]
+2347037852514.