Ku nemi watan Zul-Hijja yau Laraba, cewar Sarkin Musulmi ga al’ummar Musulmi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar musulmi da su soma duban sabon jinjirin watan Zul-hajj daga yau Laraba, 29 ga Yuli daidai da 29, Zul-ƙida, 1443 bayan Hijra.

A bayanin da shugaban kwamitin bayar da shawarwari kan lamurran addini a majalisar, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar, ya bayyana cewa za a iya kai rahoton ganin sabon jinjirin watan ga hakimi ko uban ƙasa domin isarwa ga majalisar Sarkin Musulmin.

Watan Zul-Hajj shi ne wata na 12 daga jerin watannin kalandar Musulunci, wanda a cikin sa ne al’ummar Musulmi kan gudanar da aikin Hajji da ma ibadar layya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *