Kundin Miftahul Futuhat ya zo da sabon salo a bege

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Cika da bunƙasar mawaƙi ita ce ya zamo ya shahara a dukkan salon waƙar da ya sa a gaba zai yi ta.

Sarkin waƙar Masarautar Dutse, kuma Ɗan Buran na Masarautar Gobir, Aminu Ladan Abubakar Ala, yana ɗaya daga cikin mawaƙan wannan zamani a ƙasar Hausa da Allah ya yi wa wannan baiwa.

Domin kuwa yana da baiwar shirya waƙa a kowanne ɓangarori na rayuwa wanda idan ya yi za ka ji kamar a nan fasahar sa ta ƙare, amma daga ya zo da wani salon sai kuma a ji a nan ma ya zama gwani.

Ya shahara a waƙoƙin sarakuna da kuma na jama’a, kuma ya kan ɗauki salon waƙar wani mawaƙi ya rera ta ka ji kamar shi ne ya tsara waƙar kamar yadda ya rera waƙar ‘Haɗa kanmu Afurka mu so juna’ ta Abubakar Ladan Zaria.

Sannan kuma ya yi wa kansa waƙoƙi da dama da ya rinƙa zuga kansa wanɗanda sun bada ma’ana sosai. Kamar waƙar ‘Ya aka kwana ya aka tashi mijin ‘yar Shehu Baban Zahra’. Sai kuma Waƙar ‘Shahara’, wadda ya bayar da tarihin rayuwar tun kafin ya fara waƙar zuwa lokacin da ya shahara duniya ta san da zamansa.

Wani salon waƙar da Aminu Ladan Abubakar Ala ya shahara shi ne, salon waƙar yabon Manzon Allah S A W. Duk da cewar ya yi waƙoƙi da dama na yabon Manzon Allah, sai dai babu wadda ya fi zuba basirar sa kamar a waƙar MIFTAHUL FUTUHAT. wadda kundin waƙa ne mai ɗauke da baituka dubu da ya yi wa Manzon Allah S. A.W. Kundin waƙar guda biyar ne, kuma kowanne yana ɗauke da baituka 200 ne wanda in ka haɗa kundin guda biyar zai ba ka baituka 1000 kenan.

Kundi na farko mai amshin ‘linzamin ruwata’, in da ya fara da cewa, Muhammadu Muftahul Futuhati linzamin rayuwa ta ya buɗe shi ne daɗayanta Allah, wato tauhidi, Inda ya ke cewa:

Da sunan rabbu ubanjigi mai tudawili na dare da rana. 
Da karfin iko na sa Allah a kan ce rabbul alamina. 
Da ƙarfin ƙudira ta sa Allah kum fa ya kunu ta ke gudana. 
Da ya so zartarwa buwayi a take abin nan zai gudana. 
Da ya so jera sama sama’u a cikin kwana shida tawwakana. 
Da ya so ya yi a cikin daƙiƙa za ta tashi kamar ƙiftar idona. 
Da sunan sa na ka togacewa a cikin dukkan al’ammari na. 
Da nai haka buɗi za ya samu a cikin waƙa sai ta gudana. 
To da an ji a ce ba shi ya ke ba fusahar nan in akka tona. 
Da yardar Rabbi na ke ba zata babu tsumi wayo a guna.

Sila ta salati Kali}i gun Ƙaribu masoyi a guna. 
Sila ta kaɗaita kaliƙi na a bautar Rabbi ubanjigi na. 
Silar Imani na ga Allah da annabi tsakanin arziƙina 
Sila ta shiga ta Islama ya zan hasken al’ammari na. 
Silar in San haƙƙi na Allah in bi shi in san kuɓuta da raina. 
Sila ta keyaye Hududullahi haƙƙin mai iko da raina. 
Sila ta sanin haƙƙin sahabbai da ahlullbaitinnabi na. 
Silar koyin mu da attaba’u don mu san falalar Allah gwani na.
Sila ta sanin darajar iyaye da kare mutuncin walidaina. 
Sila ta in tsarkake kaliƙina da safe da yamma Ubangiji na. 

Sai ya ci gaba da baituka na ɗayanta Allah tare da tsarkake fiffofin sa sannan ya shiga bayar da tarihin haihuwar Manzon Allah zuwa bayar da shi raino har zuwa ƙarshan kundin da ya ƙare a baiti na 200 cif. 
A kundi na biyu kuma, mai amshin ‘miƙatin rayuwa ta’. 

Wato ‘Muhammadu Muftahul Futuhati miƙatin rayuwa ta’, ya ɗora da bayar da tarihin Manzon Allah ne da zaman da ya yi a wajen Abu ɗalib baffansa da kuma irin kulawar da ya ba shi da tafiyar da ya yi da shi fatauci zuwa ƙasar Sham. da kuma zaman su a ƙasar da ma abubuwa al’jabi da suka bayyana.  

Kamar yadda suka zauna tare da malaman Kirista yake tambayar Abu ɗalib, ina mahaifin wannan yaron, sai Abu ɗalib yake sanar da shi cewa, ai ni ne babansa. 

Ya ce, “in wanda na ke nufi ne maraya zai zama a sani na.” 

Abu ɗalib ya amsa ya ce, haka ne kuwa, domin shi wannan ɗa ne a gun ɗan’uwana, dukka lamarin sa yana wajena. In da ya kammala kundin da lokacin da aka fara yi wa Manzo wahayi. 

A kundi da uku kuwa mai amshin ‘Alƙiblar rayuwa ta’. 

Wato Muhammadu Muftahul Futuhati alƙiblar rayuwa ta. Ya ci gaba da kawo ƙissar wahayi da lokacin da aka fara yi wa Manzo wahayi da kuma saɓanin da malamai suka yi wajen rana da kuma watan da aka fara yi wa Manzo wahayin. Inda yake cewa:

Amma ulama sun sa ɓa a rana da wata bisa bincike na
Waɗansu su ce a wata na Rajjab waɗansu su ce a Rammadana. 
Waɗansu su ce a Rabi’ul Auwal, amma ni na fi ga Rammadana. 
Bisa hujjar Allah ta’ala da ya yi bayani a Ƙur’ana. 
Shaharurra Rammadana lazi nuzzila fihil Ƙur’ana.
 Sannan ya ci gaba har zuwa farkon ƙisar Salmanul Farisi. 
A zango na Huɗu kuwa mai amshin Limamin rayuwa ta. 

Wato Muhammadu Muftahul Futuhati Limamin rayuwa ta ya ci gaba da kawo labarin rayuwar Salmanul Farisi da irin gwagwarmayar da ya sha domin cikar burin na haɗuwa da Manzon Allah. Sannan ya faɗa ƙissar Abu Zarril Gifari, har zuwa ƙarshan kundin 

A zango na biyar wanda shi ne kundi na ƙarshe kuwa, mai amshin ‘Jagoran rayuwa ta’. wato Muhammadu Muftahul Futuhati Jagoran rayuwa ta.

Ya ci gaba da kawo ƙissar Abu Zarril Gifari da yadda ya samu labarin bayyanar Manzon Allah har ya yi ɗamara ya nufi Makka domin haɗuwa da abin ƙaunarsa kuma mai cetonsa, in da ya ci gaba da yin baituka har zuwa cikamakin baitukan da ya tsara guda 1000 cif ba tare da ragi ba. 

Babu shakka waɗannan baitukan guda 1000 suna ƙunshe da hikimomi da nuna azanci na waƙa. 

Sannan kuma wannan kundi ne na sanin tarihin rayuwar Manzo Allah S A W. Wanda a tsaya a saurare shi ma a tsanake, wani samun ilimi ne mai faɗI. 

Sannan shi kansa tsarin waƙar an yi shi a tsanake, babu hayaniyar kaɗe-kaɗe da zai ɗauke hankalin mai sauraro daga jin saƙon da waƙar ta ke ɗauke da shi. Daman kuma irin waɗannan waƙoƙi ya kamata a samar domin sauraro ba masu kaɗe-kaɗen nanaye ba, da in kana sauraro sai ka kasa bambance kiɗan da kuma waƙar.

Allah ya ƙara wa Aminu Ladan Abubakar Ala fasahar yabon Manzon Allah da sauran waƙoƙin da yake yi na faɗarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *