Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ƙungiyoyin farar hula masu sa ido kan kadarorin Nijeriya da aka ƙwato daga hannun masu laifi sun nuna damuwa matuƙa kan yadda har yanzu ba a fara amfani da wasu maƙudan kuɗaɗe da aka dawo da su ba daga tsofaffin manyan jami’an gwamnati ba.
ƙungiyoyin sun bayyana cewa akwai dala miliyan 50 da aka ƙwato daga tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, waɗanda har yanzu ba a yi amfani da su ba, duk da cewa an tsara su don ayyukan ci gaba.
Haka kuma, sun nuna damuwa kan dala 954,000 da aka ƙwato daga tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha, waɗanda aka ce za a yi amfani da su wajen bunƙasa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar, amma har yanzu ba a ga wani aiki a fili ba.
A cewar ƙungiyoyin, duk da cewa an rattaba hannu kan yarjejeniyar dawo da dala miliyan 52.88 da ke da alaƙa da Diezani — wadda aka ware domin shirin samar da wutar lantarki ta hanyar makamashi mai sabuntawa (DARES) — har zuwa yanzu ba a fara aiwatar da shirin ba, kuma ba a bayyana inda kuɗin suke ba.
Bugu da ƙari, sun ce shekaru uku bayan dawo da kuɗaɗen da suka shafi Alamieyeseigha zuwa cikin ƙasar nan, gwamnatin jihar har yanzu tana cikin tsarin zaɓen ƙungiyoyin sa ido (NGOs) da za su kula da yadda za a aiwatar da aikin, lamarin da ya jawo tsaiko mai tsawo.
Da yake jawabi a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu kan yadda ake amfani da kadarorin da aka kwato, Daraktan Zartarwa na ƙungiyar African Network for Economic and Enɓironmental Justice (ANEEJ), Daɓid Ugolor, ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa babu wani daga cikin ayyukan da aka fara aiwatarwa har yanzu.
Ya ce da goyon bayan Ofishin Harkokin ƙasashen Waje na Birtaniya (FCDO), sun ziyarci wasu cibiyoyin kiwon lafiya da aka ware domin amfana da kuɗaɗen, amma suka tarar babu wani gagarumin ci gaba da aka samu a wuraren.
Har ila yau, ya zargi Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara ta Nijeriya da rashin bayar da cikakken bayani kan inda dala miliyan 50 da aka ware domin faɗaɗa amfani da makamashi mai sabuntawa suke.
Sai dai ya yaba wa Hukumar EFCC bisa ƙoƙarinta wajen kwato kuɗaɗen haramtacciyar hanya, amma ya jaddada cewa kwato kuɗi kaɗai bai isa ba. A cewarsa, ‘yan ƙasa na da haƙƙin sanin yadda ake amfani da kuɗaɗen da kuma waɗanda ke cin gajiyar su.
A ƙarshe, ƙungiyoyin sun buƙaci gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma hanzarta aiwatar da ayyukan da aka ware kuɗaɗen domin amfanin al’umma.
