Kuriga: Shettima ya gana da iyayen ɗaliban da aka yi garkuwa da su

Spread the love

*Ya ba da tabbacin ceto yaran cikin ƙoshin lafiya

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gana da shugabannin ƙauyen Kuriga, Jihar Kaduna da kuma iyayen ɗaliban firamaren da ɓarayin daji suka yi garkuwa da su kwanan nan a yankin.

Kusan ɗalibai 300 daga makarantar firamare da GSS da ke Kuriga cikin Ƙaramar Hukumar Chikun a jihar, ‘yan bindiga suna yi awon gaba da su a farkon makon jiya.

Sai dai a tattaunawar da suka yi a Fadar Gwamnatin Jihar a ranar Asabar, Shettima ya bada tabbacin gwamnati ta yanke shawarar ceto ɗaliban da lamarin ya shafa baki ɗaya.

Gwamna Uba Sani da sauran manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi Shettima a filin jirgin saman sojin saman da ke Kaduna.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya shaida wa gwamnatin jihar Kaduna cewa, Shugaban Ƙasa ya umarci hukumomin tsaro kan su yi dukkan mai yiwuwa wajen ceto waɗannan yara cikin ƙoshin lafiya.

Haka nan, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su kula da irin rahotannin da suke yaɗawa kan batun.

A nasa ɓangaren, Gwamna Uba Sani ya yi godiya ga Shettima bisa ziyarar da ya kai jihar da kuma ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen kuɓutar da yaran.

Kazalika, ya ce yana da yaƙinin za a ceto yaran cikin ƙoshin lafiya.

Daga nan, shi ma ya buƙaci kafafen yaɗa labari da su kiyaye labaran da za su watsa kan batun gudun kada hakan ya haifar wa ɓangaren tsaro cikas a ikinsa.

By Editor