Daga BASHIR ISAH
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tallafa wa Asusun Inganta Tsaron Jihar ɗari bisa ɗari.
Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da yake ƙaddamar da ofishin asusun a Gusau, babban birnin Jihar.
Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce Kwamitin Asusun Tsaron Zamfara na guda ne ƙarƙashin jagorancin tsohon IGP, MD Abubakar.
Idris ya ƙara da cewa, igantaccen aikin da aka yi wajen samar da ginin ofishin ya nuna himmar da Kwamitin Amintattu na asusun ke da shi wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga sauran jihohi da su yi koyi da Zamfara domin kakkaɓe matsalolin tsaron da suka addabe su.
Ya ce, “Asusun na da ayyuka da daman da zai aiwatar. Wani ƙarin aikin shi ne kawar da tunanin yara da matasa na yin rayuwa a lokutan rikice-rikice da kuma matsalar ƙabilanci a wasu wurare wanda hakan ya haifar da ‘yan fashin daji.

“Asusun wanda zai gudana ƙarƙashin jagorancin IGP M.D Abubakar (Rtd) da sauran haziƙan mambobin Kwamitin Amintattu, muna sa ran ganin amfanin asusun ga rayuwar jama’armu kamar dai yadda kuka yi a fannoninku.
“Mun damƙa muku wannan amanar saboda muna da yaƙinin za ku iya. Muna godiya ga.e da hidimarku ga jiharku,” in ji Lawal.
