Daga USMAN KAROFI a Abuja
Wani kwale-kwale mai ɗauke da mutum sama da 35 ya kife a rafin Rima da ke yankin Dundaye a ƙaramar hukumar Wamakko a Jihar Sokoto.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Sokoto ta bayyana cewa zuwa yanzu an samu gawar mutum ɗaya yayin da wasu 15 su ka ta so da kansu daga cikin ruwan.
Tuni dai ƙungiyar Red Cross tare da mai ba wa gwamna shawara kan al’amuran gaggawa suka halarci inda wannan abu ya faru.
Kwale-kwalen ya kasance ɗauke da mafi yawa yara, mata da tsofaffi a ƙoƙarin su na tsallakawa domin su je gona.
Sai dai wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne saboda mutane sun yi yawa a saman shi.
