Wasu ɓatagari sun cinna wa coci wuta a Kontagora

Spread the love

Wasu ɓatagari sun cinna wa cocin Redeemed dake kan titin Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) a Kontagora, Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar.

Jaridar Blueprint ta rawaito cewa, irin wannan lamarin ya taɓa faruwa shekaru goma da suka gabata, wasu ɓatagari sun yi amfani da rikicin da ya afku a yankin suka cinna wa cocin wuta, kuma daga bisani aka gargaɗi shugaban cocin kada ya sake ginawa.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Neja, Rev. Dr. Bulus Dauwa Yohanna, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa cocin, inda ya bayyana shi a matsayin ta’addanci kuma ba daidai ba.

Ya ce, “Akwai ‘yancin addini a Jihar Neja, sannan yayi kira da gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki mataki domin yin hakan zai taimaka wajen magance duk wani nau’in rikici da zai iya faruwa.

By ukarofi