Kwamishinan Gombe ya gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi kan gaskiya da riƙon amana

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Kwamishinan ƙananan hukumomi da raya al’umma na Jihar Gombe, Sani Ahmed Haruna, ya buƙaci sabbin shugabannin ƙananan hukumomi da na cibiyoyin raya ƙananan hukumomi (LCDAs) su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya, riƙon amana da kuma kula da dukiyar jama’a yadda ya kamata.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron farko na kwamitin raba kuɗaɗen ƙananan hukumomi (JAAC) tare da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Gombe.

A cewarsa, al’ummar jihar sun ɗora wa shugabannin alhakin kawo ci gaba a matakin ƙasa, don haka ya buƙace su su tabbatar da amincewar da aka ba su ta hanyar shugabanci nagari da aiwatar da ayyukan da za su amfani jama’a.

Haruna ya kuma isar da saƙon Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, inda ya buƙaci shugabannin su kasance masu himma wajen aiki, su rungumi gaskiya da riƙon amana tare da tabbatar da isar da ayyukan gwamnati cikin inganci.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ƙananan hukumomi da LCDAs domin inganta ayyukan gwamnati, tare da umartar cewa duk wata buƙata ko wasiƙar hukuma ta bi ta hannun sakatarorin ƙananan hukumomi ko mataimakinsu bisa ƙa’idojin aiki.

Haka kuma, ya shawarci shugabannin da su riƙa adana bayanan ayyukan hukuma da kuma kare muhimman takardun gwamnati domin ƙarfafa tsarin gudanarwa.

Tun da farko, babban sakataren ma’aikatar, Shuaibu Ibrahim, ya taya shugabannin murnar zaɓensu tare da tabbatar musu da goyon bayan ma’aikatar wajen aiwatar da manufofin gwamnatin jihar.

A yayin taron, daraktan Baitul Mali ya gabatar da rahoton rabon kuɗaɗen wata da yadda aka kashe su, yayin da taron ya samu halartar shugabannin ƙananan hukumomi da na LCDAs, daraktocin ma’aikatar da sauran manyan jami’an gwamnati.

By ukarofi

Leave a Reply