Kwamishinan ‘yan sandan Katsina ya umarci jami’ansa su himmatu wajen inganta tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Katsina CP Aliyu Abubakar Musa yayi wani taron gaggawa da manyan jami’an ‘yan sanda na hedkwata da na ƙananan hukumomin domin duba yadda suke gudanar da harkokin tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa taron ya zama dole ganin yadda a ke samun yawaitar ƙaruwar satar wayoyin wutan lantarki a faɗin jihar da yace haka na faruwa ne sakamakon ƙarancin wutan lantarki.

Kwamishinan yayi gargaɗin cewa rundunar ‘yan sanda ba zata zuba ido ta ga wasu ɓata gari na yin zagon ƙasa da lalata kayan hukumar wutan lantarki a jihar ba.

CP Aliyu Abubakar ya bayyana cewa taron zai duba yadda rundunar ta ke tafiyar da harkar tsaro da kuma fidda wasu sabbin tsare tsare da zai inganta samar da tsaro a faɗin jihar.

Ya kuma faɗa cewa jami’an sa zasu sa ido ga duk kaddarori na hukumar wutan lantarki da fitillu na manyan hanyoyi domin samar da tsaro a wuraren yayin da ake tunkarar hutu da bukukuwan ƙarshen shekara.

Ya buƙaci jami’an tsaron da su maida hankali wajen sa ido tare da tattara bayanai don kare lafiya da dukiyar al’umma da kuma ɗaukan matakin gaggawa in sun sami rahoton ko ta kwana.

Kwamishinan ya kuma umurce su da su haɗa kai da hukumar samar da wutan lantarki a jihar don bada tsaro na musamman akan kaddarorin hukumar a faɗin jihar .

Haka kuma ya buƙaci manyan jami’an tsaron na ƙananan hukumomi da su haɗa kai da sarakunan gargajiya da shugabannin alummomin da ‘yan banga da ke yankunan su domin tabbatar da tsaro a yankunan su.